✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar wa Kefas Agbu na PDP kujerar Gwamnan Taraba

Alkalin ya kori karar da cewa kotun ba za ta bata lokaci wajen sauraron korafin ba.

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da Kefas Agbu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Taraba.

Kotun ta kori karar da dan takarar jam’iyyar NNPP, Muhammad Yahaya ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar da Gwamna Kefas ya samu.

Peter Afen, alkalin da ya yanke hukuncin, ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar NNPP ya gaza gabatar wa da kotun gamsasshiyar hujja kan karar da ya daukaka.

Kan haka ne alkalin ya kori karar da cewa kotun ba za ta bata lokaci wajen sauraronsa ba.