Wasu matasa sun kashe wani dan sanda da yake kokarin raba fada tsakanin wasu kungiyoyi da ba sa ga-maciji da juna a Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja.
Dan sandan wanda aka bayyana sunansa da Nasiru, an kashe shi ne a kauyen Manima na gundumar Gaba da ke yankin.
- Ciwon zuciya na kama ’yan Najeriya 80,000 duk shekara – Masani
- NAJERIYA A YAU: Gayyatar ’yan IPOB Legas tamkar gayyatar ’yan Boko Haram ne – Lauya
Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya bayan barkewar rikicin, an gayyato jami’an tsaro, inda bayan zuwansu, sai mambobin kungiyoyin suka sare shi da makamai a ka.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa kafin faruwar lamarin, dan sandan ya halarci wani taron zama lafiya a kauyen Doko na Karamar Hukumar ta Lavun, inda aka tattauna batun yawan faruwar rikice-rikice kan filaye a yankin.
Ya ce, “Yanayin yadda ake yawan samun matsalar rikici tsakanin mutanen yankinmu a ’yan kwanakin nan abun takaici ne. Kuma galibi ana yi ne ko dai a kan filaye ko kuma sarautu.
“Ko gabanin kisan dan sandan, sai da ya halarci wani taron zaman lafiya a kauyen Doko, kafin rikicin ya barke a Manima, inda suka je su shiga tsakani.”
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce tuni suka kama mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin.