✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan sanda ya kashe abokan aikinsa 4 a Indiya

Ya bude musu wuta da tsakar dare a wurin aiki.

Wani dan sanda ya bindige abokan aikinsa hudu ya kuma jikkata wasu uku a wurin aiki ranar Litinin a kasar Indiya.

Dan sandan wanda ke aiki a runduna ta musamman ta CRPF ya yi wa abokan aikin nasa ruwan albarusai ne a birnin Chhattisgarh, inda ya kashe hudu daga cikinsu.

Gidan talabajin na NDTV na kasar Indiya ya ruwaito cewa dan sandan ya yi aika-aikan ne a sansanin bataliya ta 50 ta rundunar CRPF da ke kauyen Linganpalli da misalin 3:15 na dare.

NDTV ya ruwaito cewa an kaddamar da bincike kan musabbabin harbin da dan sandan mai mukamin Kwanstebul, mai suna Reetesh Ranjan .