Wani dan sanda ya bindige abokan aikinsa hudu ya kuma jikkata wasu uku a wurin aiki ranar Litinin a kasar Indiya.
Dan sandan wanda ke aiki a runduna ta musamman ta CRPF ya yi wa abokan aikin nasa ruwan albarusai ne a birnin Chhattisgarh, inda ya kashe hudu daga cikinsu.
- Sai an shekara 120 kafin Najeriya ta samu wadatattun likitoci
- Motar hukumar kiyaye hadurra ta yi hatsari, ta kashe mutum 2 a Bauchi
Gidan talabajin na NDTV na kasar Indiya ya ruwaito cewa dan sandan ya yi aika-aikan ne a sansanin bataliya ta 50 ta rundunar CRPF da ke kauyen Linganpalli da misalin 3:15 na dare.
NDTV ya ruwaito cewa an kaddamar da bincike kan musabbabin harbin da dan sandan mai mukamin Kwanstebul, mai suna Reetesh Ranjan .