Hukumar ’yan sanda ta tabbatar da labarin harbin da wani jami’inta ya yi wa fitaccen jarumi kuma daraktan fina-finan Nollywood, Azeez Ololade Ijaduade, a wurin casu a Jihar Ogun.
Labarin harbin harbin ya bazu a shafukan sada zumunta ne a daren Asabar bayan da abokin aikin jarumin, Abiodun Adebanjo ya wallafa Instagram cewa: “Wani dan sanda Najeriya sun harbe darakta na, Azeez Ijaduade.
“A halin yanzu dan jarumin yana cikin mawuyacin hali a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Babcock; Duk wanda ke da lambar IG ko kwamishina ya taimaka.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya bayyana cewa kwanson harsashi ne — ba harsashi ba — ya sami jarumin a wuya.
- Yadda Emefiele ya mallaki bankuna 3 ta barauniyar hanya
- CBN ya janye haramcin amfani da kudaden Crypto
- Zaben Kano: Dahiru Bauchi ya nesanta kansa da wasikar ‘Neman Adalci’
Ya ce, “A casun karshen shekara na Kamfanin Bramaj a wani otal ne wani dan sandan kwantar da tarzoma ya yi harbi iska, amma abin takaici sai kwanson harsashin ya samu wani jarumi mai suna Azeez Ijaduade a wuya.
“An garzaya da shi asibiti a Ilishan kuma yana samun sauki.”
Odutola ya kara da cewa an kama jami’in da ya yi harbin kuma an fara bincike kan lamarin.