✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Emefiele ya mallaki bankuna 3 ta barauniyar hanya

Rahoton ya tona yadda Emefiele ya saye bankuna biyu ba tare da ya kashe ko sisi ba

An bankado yadda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya saye bankunan Union, Keystone da Polaris ta barauniyar hanya.

Wani rahoto da mai bincike na musamman da shugaba Bola ya nada, Jim Obazee ya tona yadda Emefiele ya mallaki bankin Keystone da bankin Polaris ba tare da biyan ko sisi ba.

Rahoto ya bayyana yadda wani aminin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, marigayi Alhaji Ismaila Isa Funtua da Emefiele suka saye bankuna biyu ba tare da biyan ko sisi ba.

A cewar rahoton da Jim Obazee ya mika wa Shugaba Tinubu a ranar 20 ga Disamba, Emefiele ne ya saye bankunan Union.

Aminiya ta samu wadannan bayanai ne daga wasu takardu daga majiya mai tushe, amma har yanzu ba a bayyana sakamakon binciken a ga jama’a a hukumance ba.

Amma gwamnatin tarayya ta ce za ta kwace bankunan biyu da Emefiele ya saya a kan farashi mai rangwame.

“Mun kammala bincike kan wannan ciniki kuma muna dab da dawo da wadannan bankuna biyu ga gwamnatin tarayya,” in ji rahoton.

An dakatar da Emefiele ne kwanaki kdan bayan hawan Tinubu kan karagar mulki.

Jim kadan da sallamar sa ne jami’an tsaro suka kama shi tare da tsare shi bisa zargin sa da laifin zamba.

Daga bisani shugaban kasan ya umarce su da hukumomin yaki da rashawa su binciki ayyukan CBN a karkashin jaogarcin Emefiele.

A ranar Asabar aka sako Emefiele daga gidan yari bayan ya cika sharuddan beli ciki har da biyan Naira miliyan 300.

Lauyoyinsa sun ki cewa komai game da badakalar sayar da bankunan.

Hakalika mai magana da yawun gwamnati bai amsa bukatarmu ta neman karin bayani ba.