✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Ronaldo ya zura kwallaye hudu a wasansa na farko

Dan Cristiano Ronaldo da ake kira Ronaldo Junior, ya yi nasarar zura kwallaye hudu a raga a wasansa na farko  a kulob din Jubentus na…

Dan Cristiano Ronaldo da ake kira Ronaldo Junior, ya yi nasarar zura kwallaye hudu a raga a wasansa na farko  a kulob din Jubentus na yara da ke Italiya.

Idan za a tuna, a makon jiya ne muka ruwaito yadda dan Ronaldon ya samu nasarar sanya hannu a kulob din Jubentus na yara na ’yan kasa da shekara 9.

A karshen makon jiya ne yaron ya samu nasarar zura kwallaye hudu a raga a wasansa na farko da hakan ya ba magoya bayan kulob din sha’awa da kuma mamaki.   Hakan ya nuna  akwai alamar yaron zai gaji mahaifinsa  Cristiano Ronaldo wajen shahara a fagen kwallon kafa a fadin duniya.

Sai dai Ronaldo wanda shi ma ya canza sheka zuwa kulob din Jubentus na manya a kakar wasa ta bana, kawo yanzu bai samu nasarar zura ko kwallo daya a raga a gasar Serie A ta Italiya ba wacce aka fara kimanin makonni uku da suka gabata.

Masoya kwallon kafa da dama sun yaba wa  Ronaldo Junior a bisa kokarin da ya yi na zura kwallaye hudu a raga a wasansa na farko.