✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Ronaldinho ya sanya wa kulob din Cruzeiro hannu

Amakon jiya ne Joao Mendes dan Ronaldinho, ya samu nasarar sanya wa kulob din Cruzeiro na matasa hannu a Brazil. Saurayin dan shekara 14, ya…

Amakon jiya ne Joao Mendes dan Ronaldinho, ya samu nasarar sanya wa kulob din Cruzeiro na matasa hannu a Brazil.

Saurayin dan shekara 14, ya samu nasarar sanya hannu a kwantaragi ne bayan kulob din ya yi masa gwaji inda ya amince da kwazon da ya nuna.

Sai dai rahotannin da ke fitowa sun nuna matashin a lokacin da ya je kulob din don yin gwaji, bai bayyana wa kowa cewa Ronaldinho, shahararren dan kwallon duniya ne mahaifinsa ba.  Ya je ne a kashin kansa ba tare da neman taimakon wani ba.

A yayin gwajin Joao Mendes ya kasance a sahun farko na ’yan kwallon da suka fi nuna kwazo.

A sanarwar da kulob din Cruzeiro ya fitar jim kadan bayan ya kulla yarjejeniya da matashin, an nuna Mendes yana da baiwar buga kwallo inda ya cancanci yin kwallo a kowane bangaren fili musamman a tsakiyar fili ko gaba ganin yadda Allah Ya hore masa tsawo da gudu da kuma iya lailaya kwallo.

Kulob din ya ce a yayin kulla yarjejeniyar ce ya fahimci ashe Mendes dan Ronaldinho ne, abin da ya ba su mamaki, ganin yadda yaron ya nuna kwazo ba tare da ya nemi taimakon mahaifinsa ko wani kafin a dauke shi ba.

Shi ma Ronaldinho a wata hira da aka yi da shi ya ce bai san lokacin da dansa ya halarci wajen yin gwaji da kulob din Cruzeiro ya gayyaci matasan ’yan kwallo ba balle a ce zai nemi wani taimako daga wajensa.  Sai dai ya yi wa dan nasa fatan alheri wajen samun daukaka a fagen kwallo kamar yadda shi ma ya samu.

Ronaldinho dai ya taba zama Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya. Kuma ya buga wa kulob da dama da suka hada da FC Barcelona na Sifen da Inter Milan da AC Milan da ke Italiya da sauransu.

Rahotanni sun ce tuni Ronaldinho ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa kuma ya rungumi harkar siyasa a Brazil.