Wani likita dan Najeriya Dokta Onyema Ogbagu ne ya kirkiro rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer na kasar Amurka ya samar.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da haka, tare da cewa rigakafin shi ne mafi inganci kuma na farko da aka samar a Amurka domin cutar COVID-19.
- Dukan dan takara: Kotu ta sa a kamo Shugaban Karamar Hukumar Gaya
- COVID-19: Gidauniyar TY Danjuma ta raba tallafin N107m a Neja
- An sace dan uwan Ministan Noma Sabo Nanono
“‘Yan Najeriya sun ba wa duniya gudunmuwa ta fuskoki da dama. Muna matukar jinjina ga Dokta Onyema Ogbuagu da ya taimaka aka samar da rigakafin COVID-19”, inji Ofishin.
Ofishin jakandancin ya sanar da haka ne ta shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Dokta Onyema ya yi digirinsa na farko ne a Jami’ar Kalabar a shekarar 2003, kuma Farfesa ne a fannin da ya shafi magani da cuttuka masu yaduwa a Jami’ar Yale da ke Amurka.