An haifi wani dan maraki da hanci hudu da idanu uku inda mutanen yankin suka ce sun yi imani cewa wannan halittar mu’ujiza ce daga Allah.
Wadansu jama’ar kasar Indiya na ganin haihuwar dabba mai wata halittar al’ajabi za ta kawo wadata ga mazauna garin da aka haife ta, inda da yawa sukan yi wa dabbar kyaututtukan su kwakwa da furanni.
- Harin ISIS a gidan yarin Siriya ya illata mutum 45,000
- Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘farfaganda’
An haifi dan marakin ne a jinsin da aka tabbatar ya fi kowane jinsin shanu yawan madara a wata gona da ke birnin Rajnandgaon a Jihar Chhattisgarh ta kasar Indiya, inda mazauna yankin ke yin layi don ziyartar marakin a matsayin ‘dabba mai tsarki’.
Manomi Neeraj Chandel ya yi ikirarin cewa, mutane da yawa sun yarda cewa marakin da suke yi wa lakabi da Hindu God Shiba, wanda kuma aka fi sani da Ubangijin shanu.
A cikin wasu hotuna da bidiyo, ana iya ganin marakin da ido na uku a goshinsa da hanci hudu. Neeraj ya ce: “Da saniyar ta haihu, sai muka dauka wani rauni ne a goshinsa kafin mu gane cewa gurbin ido ne bayan yin amfani da tocila don haskawa da kyau.
Daga nan ne muka gano hanci hudu wanda hakan ya sa mutanen garin suka cika gidanmu da daddare.
Dan marakin yana motsi kuma yana shan nonon mahaifiyarsa kuma yana amfani da ido na uku a goshinsa da kyau. Kamar dai Allah ne Ya kawo mana dauki,” inji shi.
Marakin yana da nauyin kilo 30 kuma yana da dogon harce fiye da matsakaicin dan maraki, kuma har yanzu yana shan madara a-kai-a-kai.
Mazauna yankin sun yi imani cewa haihuwar irin wannan dabba na kawo sa’a da wadata ga mazaunansa, inda da yawa suka yi ta yi wa dabbar kyaututtukar kwakwa da furanni.
Wannan ba shi ne dan maraki na farko mai idanu da yawa da aka taba haifa ba.
A watan Mayun 2021, wani dan maraki mai ido uku ya isa birnin Brynmawr, a yankin North Wales.
Ba a yanka saniya ko dan maraki a Indiya, kuma har yanzu ba a tabbatar da makomarsa ba, domin wani jami’in ma’aikatar kiwo ya yi imanin cewa, dabbar ba za ta dade a raye ba.
Sun ce, “A wadannan lokuta ba kasafai ake samun hakan ba, amma irin wadannan dabbobin da ba su dadewa a raye . Ko dai su yi rayuwa mai tsawon wata 24 ko kuma za su iya mutuwa cikin wasu makonni.”
Neeraj ya tuntubi wani likitan dabbobi na gida don duba lafiyarsa wanda ya tabbatar da cewa duk da sauye-sauyen da ba a saba gani ba, a halin yanzu marakin mai ido uku yana cikin koshin lafiya.
Manomin ya kuma tabbatar da cewa, saniyar da ta haifi marakin tana cikin koshin lafiya. Ya kara da cewa: “Kafin ta haihu, ta haifi ’yan maruka guda biyu, lafiyayyu ba tare da wani sauyin halitta ba.”
Dangane da bayyanar da ba a saba gani ba, likitan ya tabbatar da sauyin halittar saniyar yana zuwa lokacin kimiyya.
Wata likita mai zaman kanta, Madan Anand, ta ce: “Haihuwar marakin wani lamari ne na nakasa. Ba ya da alaka da camfi ko a yi imani.
“Ya kamata a wayar da kan jama’a, musamman wadanda suka fito daga kauyuka da suka saba bautar irin wadannan dabbobi,” inji ta.
Likitar dabbobin ta bukaci a gudanar da gangamin wayar da kan jama’a don guje wa irin wadannan ayyuka.
Duk da mutane da yawa suna ganin bayyanar dan maraki a matsayin abin al’ajabi, likitar dabbobin ta ci gaba da cewa dalilin nakasar shi ne sakamakon sauyin kwayar halitta kafin haihuwa.
Mutane daga mutanen yankin sun nuna cewa, dan marakin yana da matukar muhimmanci.
Har yanzu yana kokarin ya tsaya a kan kafafunsa kamar yadda sauran maruka suke yi bayan haihuwarsu. Amma jama’ar da suka taru sun nuna yana da matukar ma’ana.