✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan kwallon Zamalek zai kai kulob din kara gaban Hukumar FIFA

Mahmoud Abdul Razek Shikabala dan kwallon kulob din Zamalek da ke Masar ya yi barazanar kai kulob din gaban Hukumar shirya kwallo ta duniya FIFA…

Mahmoud Abdul Razek Shikabala dan kwallon kulob din Zamalek da ke Masar ya yi barazanar kai kulob din gaban Hukumar shirya kwallo ta duniya FIFA muddin ba su biya shi albashin da yake binsu na zunzurutun Dala dubu 800 kwatankwacin Naira Miliyan 123 ba.
Mahmoud Abdul Razek dai ya zuwa ranar Talatar da ta wuce ya shafe kimanin kwanaki shida ba tare da ya halarci sansanin horar da ’yan kwallon kulob din ba don nuna bacin ransa a kan basussukan da yake bin kulob din.
“Mun tuntubi mahukunta kulob din Zamalek a kan batun biyan albashin Shikabala amma ya zuwa wannan lokaci ba su ce mana komai ba”, inji ejent din dan kwallon mai suna Samir Abdul Tawab a lokacin da yake hira da kafar sadarwa ta Supersport.com.
“Mun sake rubuta wa mahukunta kulob din wasika a karo na biyu idan ba su yi wani abu a kai ba ko shakka babu za mu kai kara gaban Hukumar FIFA don ba mu izinin raba-gari da kulob din”.
Al’amarin rashin biyan albashi a kulob din Zamalek ba sabon abu ba ne, don tuni dan kwallonsu mai suna Ahmed Eid shi ma ya shiga yajin aiki a kan rashin biyansa albashi da alawus-alawus da yake bin kulob din.
Kafar sadarwar Supersport.com ta kalato cewa tuni Kocin kulob din Helmy Tolan ya tattauna da shugaban kulob din na Zamalek Kamal Darwish don ganin an shawo kan wannan matsala don ganin an warwareta kafin a fara kakar wasa ta bana a karshen wannan wata.