✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan kwallon Najeriya ya auri jarumar Kannywood

Jarumar ta fara fina-finan Hausa tana da 'yar shekara 10 a duniya.

Dan Wasan Kwallon Kafar Najeriya, Abdullahi Shehu mai taka leda a kungiyar Omonia Nicosia da ke kasar Cyprus, ya auri jarumar Kannywood a ranar Juma’a.

Dan wasan dai ya auri jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Naja’atu Muhammad Suleiman wacce aka fi sani da Murjanatu ’Yar Baba.

  1. Dubun masu fashi a na’urar POS 2 ta cika a Kogi
  2. ‘’Yan bindiga na hada baki da sojoji’

An daura auren dan wasan da jarumar a masallacin Umar Bin Kattab da ke cikin birnin Kano bayan idar da sallar Juma’a, kuma an biya N50,000 a matsayin sadaki.

Amarya Naja’atu Muhammad Suleiman da Ango Shehu Abdullahi

Naja’atu ta fara fitowa a fina-finan Hausa tun tana da shekara 10 a duniya.

Ta fito a cikin fina-finai da suka hada da ‘Harira’, ‘Hakkin rai’, ‘Auren gaja’ da dai sauransu.

Dubban mutane ne suka sami halartar daurin auren dan wasan, ciki har da dan wasan gaba na Najeriya, Ahmed Musa.

Shehu Abdullahi da Ahmed Musa, bayan daura auren
%d bloggers like this: