✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Najeriya Audu Seriki ya rasu a hadarin mota

Dan kwallon Najeriya da yake buga wa kulob din Lobi Stars ya rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da shi a ranar 20…

Dan kwallon Najeriya da yake buga wa kulob din Lobi Stars ya rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da shi a ranar 20 ga watan nan da muke ciki.
Hadarin ya rutsa da shi ne a lokacin da suke kan hanyar tafiya garin Bauchi daga Jihar Yobe tare da matarsa da kuma ’yarsa.
Sai dai rahoton ya ce dan kwallon ne kawai ya rasu a hadarin yayin da matarsa da kuma ’yarsa suka tsira.
Tuni mahukunta kulob din Lobi Stars suka tabbatar da wannan labari kuma sun aika da sakon ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin.
“A gaskiya mun yi bakin cikin rabuwa da dan kwallonmu Audu Seriki a wannan lokaci da muke tsananin bukatarsa, kuma yana daga cikin ’yan kwallon da suke taimakawa kulob din Lobi wajen samun nasara”, inji sanarwar da kulob din ya fitar.