Tsohon dan kwallon kasar Ghana, Raphael Dwamena, ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin da yake tsaka da buga wasa a kasar Albaniya.
Dan wasan mai shekara 28 ya kasance a gaba wajen zura kwallo a raga a gasar Albaniya a kakar wasa ta bana, inda ya jefa wa kungiyarsa, Egnatia kwallaye tara.
- Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga sun ceto mutane a Katsina da Kaduna
- An cafke matar da ta sace ’yar shekara 3 a Neja
Dwamena ya jefa wa Ghana kwallo tara, amma ya sha fama da ciwon zuciya tsawon rayuwarsa.
A 2017, yunkurinsa komawa kungiyar kwallon kafa ta Brighton ya gagara, bayan ya gaza tsallake matakin gwajin lafiya a kungiyar, kuma a 2021 ya fadi ana tsaka da wasa a Austria.
Mai sharhi kan harkokin kwallon kafa na Albaniya, Endi Tufa, ya ce Dwamena “ya rayu ne don kwallon kafa”.
An yi masa aiki a zuciya a 2020, inda aka dasa na’ura don ba shi damar ci gaba da murza leda.
Bayan yi masa aiki, ya koma taka leda a gasar Danish, Austria, da Swiss kafin daga bisani ya koma kungiyar Albaniya KF Egnatia a watan Janairun bana.
Hukumar kwallon kafa ta Albaniya ta ce mutuwarsa ta girgiza harkar kwallon kafar kasar kuma ta dage duk wasannin da aka shirya yi a kasar a wannan mako.