✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga sun ceto mutane a Katsina da Kaduna

Jami'an tsaro sun kashe ’yan bindiga shida tare da kwato makamai a jihohin Kaduna da Katsina

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga shida tare da kwato makamai a jihohin Kaduna da Katsina.

A Jihar Katsina ’yan sanda sun hallaka ’yan bindiga uku suka kuma ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a yankin Gogalo da ke Karamar Hukumar Jibia.

Maharan sun shigo kauyen ne dauke da muggan makamai, inda suka sace mutum uku.

Daga bisani ’yan sanda suka bi sawu, suka hallaka uku daga cikinsu sannan suka kwato wadanda aka sacen.

A Jihar Kaduna, sojojin sun hallaka ’yan bindigar ne a yankin kananan hukumomin Kajuru da Birnin Gwari na jihar.

Sun kuma kama bindigogi kirar AK47 da sauran makamai da wayoyi, wasu kuma suka tsere da raunukan harbi.