A makon jiya ne wani abin tsautsayi ya fada wa wani dan kwallo a Indiya a lokacin da yake taka-juye saboda nasarar da ya samu ta zura kwallo a raga. dan kwallon ya samu karaya a wuyansa da kuma a kashin bayansa ne jim kadan bayan ya zura kwallo a raga a daidai minti na 63 da hakan ta sa shi yin taka-juye.
Wannan al’amarin ya faru ne a Arewa maso Gabashin Indiya. dan kwallon mai suna Peter Biaksangzuala ya zura kwallo ne a daidai minti na 62 a lokacin da kulob dinsa Bethelehem benghlang FC ya kara da na Chanmari West FC a gasar rukunin ’yan dagaji.
Rahoton da kafar sadarwar Gulfnews.com ta kalato ya nuna dan kwallon ya gamu da tsautsayi ne a lokacin da yake yin taka juye al’amarin da ya sa ya fado da kai kuma nan take ya karya wuya da kasahin bayansa.
Rahoton ya ce abokansa da ke buga kwallo da sauran jami’an da ke kula da yadda wasan ke gudana ne suka garzaya da shi wani asibiti mafi kusa amma kwana biyar bayan an kwantar da shi ne rai ya yi halinsa.
Sakataren Hukumar kula da shirya gasar kwallo a garin Nizoram ya bayyana al’amarin a matsayin tsausayi da kuma takaici. “A gaskiya mun kadu matuka da faruwa wannan al’amari. Marigayin dan kwallo ne mai kwazo da ake masa hasashen zai yi kwallo a gasar rukuni-rukuni ajin kwarru a nan gaba saboda kwazonsa. Mutuwarsa ta girgiza mu don da farklo mun dauka zai warke ya cigaba da yin kwallo amma kwatsam sai muka samu labarin ya mutu”, inji shi a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.
dan kwallo Peter dai ya rasu ne yana da shekara 23, kuma an shaide shi a matsayin wanda ya kware a wajen yin taka-juye a duk lokacin da ya zura kwallo a raga. A wannan karo ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado da ka a lokacin da yake taka-juye jim kadan bayan ya zura kwallo a raga.