Wani rikakken dan daba mai suna Hamidu Mukhtari, wanda aka fi sani da Dogo, ya lakada wa wani dan jarida dukan kawo wuka a cikin gidan gwamnatin Jihar Adamawa da ke Yola.
Dan jaridar, mai suna Ibrahim Mista Ali, an ce ya kwashi kashinsa a hannu ne bayan ya soki lamirin Gwamnan Jihar, Ahmadu Umaru Fintiri.
- Cin Zarafin Shehunnai: Mai Dubun Isa ya janye kalamansa
- Sojojin Nijar sun bukaci a fitar da jakadan Faransa ta karfin tsiya
Dan jaridar dai ya gamu da bacin ranar ne lokacin da ya je ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar domin wani taron manema labarai, inda a nan ne Dogon ya yi masa kwanta-kwanta.
Rahotanni sun nuna cewa daman a baya dan dabar ya taba yi wa dan jaridar barazana har sau biyu, saboda wallafa wasu abubuwa da ba su yi wa gwamnatin dadi ba.
A cewar dan jaridar, “Ya mare ni, ya naushe ni har sau biyu sannan ya ci min kwala a gaban jami’an tsaro, wadanda daga bisani suka shiga tsakani sannan suka roke shi ya sake ni. Ya lashi takobin cin zarafina saboda na dauki rahotannin ‘yan adawa.”
An yi amannar Dogo ya sha jagorantar kai wa mutane da dama hari, wadanda ya yi wa zargin nuna adawa ga gwamnati.
Bugu da kari, dama jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun taba kama dan dabar kan zargin safarar miyagun kwayoyi, kuma yanzu haka ma belinsa kotu ta bayar.
Da wakilinmu ya tuntubi Sakataren Yada Labaran Gwamna Fintiri, Humwashi Wonosiko, ya ki cewa komai a kan lamarin, inda ya ce ba shi da alaka da gwamnati, fada ne kawai tsakanin mutum biyu.