Aminiyar matashiyar nan mai suna Ummukulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita da wani dan kasar China, Geng Quanrong ya kashe a Jihar Kano, ta yi karin haske dangane da alakar mutanen biyu da lamarin ya shafa.
A wata zantawa ta musamman da ta yi da Aminiya, Rabi’a N. Garba, ta ce sai da Mista Geng ya karbi addinin Islama sannan marigayiya Ummita ta amince ta fara soyayya shi da zummar za su yi aure.
- El-Rufai ya so a kai Film Village Kaduna, amma… —Sani Mu’azu
- Kotu ta ci Sheikh Abduljabbar tarar Naira miliyan 10
Aminiya ta ruwaito cewa, a halin yanzu dai Mista Geng yana ci gaba da bai wa diddigensa hutu a hannun jami’an tsaro da tuni suka yi ram da shi.
Bayanai sun ce, ’yan unguwa ne dai suka rike dan Chinar tare da mika shi ga jami’an tsaro bayan ya kashe matashiyar mai shekara 23 a gidan iyayenta a ranar Juma’ar makon jiya.
Rahotanni sun bayyana cewa, marigayiya Ummita dai bazawara ce wadda suka rika shan soyayya da dan Chinar tun kafin aurenta, kuma alakar ta ci gaba har bayan ta shiga gidan miji, lamarin da ake zargi shi ya yi sanadiyar mutuwar aurenta.
Abu kadan ke bata masa rai —Rabi’a
Rabi’a N. Garba wadda ta ce ita ce babbar kawar marigayiyar, ta shaida wa Aminiya cewa, a iya saninsu da dan kasar Chinar, sunansa Frank, kuma ya sanar da su ya mayar da sunansa Faisal bayan ya yi musu ikirarin karbar addinin Islama.
“A iya sani na da shi, mutum ne da abu kadan ke bata masa rai, don ko jinkiri aka yi ba a ba shi amsa ba idan ana chatting sai ya harzuka.
“Abun da na sani shi ne cewa alakarsu da ita [Ummita] soyayya ce ko kuma ma na ce kawance, don ita kanta [Ummita] ta san ba za ta taba aurensa ba.
“Ta yi duk iya kokarin da za ta yi don ya daina kulata amma daga bisani da lamarin ya ci tura ta ga cewa nacin nasa ya yi yawa, sai ta ba shi dama suka fara soyayya saboda ya ce da ita zai musulunta in dai hakan zai sa ya samu karbuwa a wurinta.
“Bayan ya ce mana ya musulunta ne saboda ita [Ummita], shi ya sa ta amince ta fara soyayya da shi, har ta kai ya fara koyon yadda ake yin Sallah,” a cewar Rabi’a.
Dangane da alakar dan Chinar da marigayiya Ummita, Rabi’a ta ce, “Ummita aminiya ta ce, kuma tana da faran-faran ga duk wanda ya rabe ta.
“Tana da kyakkyawar alaka da mutane kuma ba zan taba iya mantawa da ita ba a rayuwata.
Ta yi aure a watan Fabrairun wannan shekara, kuma tun kafin nan, an hana ta auren dan Chinar saboda iyayenta da danginta ba su yarda da akidarsa ta karbar addinin Islama duk da ya yi ikirarin ya musulunta.
Akwai wani lokaci da muka yi chattinga da shi kuma muka gano bai sauya sunansa na Frank da muka san shi da shi ba duk da ya ce mana ya mayar da sunansa Faisal.
Sai muka tambaye shi kan me ya sa yake amfani da tsohon sunansa na Frank bayan ya sanar da mu cewa ya musulunta kuma ya mayar da sunansa Faisal.
Sai muka gano ashe duk maganar da ya fada mana karya ya yi, saboda bai daina amfani da suna Frank ba, kuma ba mu san shi da wani suna Geng ba don bai taba fada mana wannan sunan ba.
Ya kuma fada mana cewa shi dan kasuwa ne da yake harkokinsa a kasuwar Kantin Kwari.
Sai aka fada masa cewa ya rabu da ita don tasu ba za ta taba zuwa daya ba a wurin danginta.
Ya amince ya rabu da ita, kuma daga baya ta samu miji har ta yi aurenta, amma Allah Bai kaddara auren zai jima ba.
Ba mu taba tsammanin cewa bai hakura da ita ba, ashe ya yi bincike ya gano aurenta ya mutu kuma ta dawo gidan iyayenta.
Ta sha yi min korafi a kan yana damunta, har na ce ta hakura da shi kuma ta nemi Allah-Annabi ya fita daga rayuwarta.
Akwai wasu lokuta da yak rika turo min sakonni ta shafina na Instagram yana fada min cewa har yanzu fa bai daina sonta ba duk da tana gidan miji, sai na sanar da shi cewa wannan abun da yake yi ya ci karo da al’adunmu.
Bayan aurenta ya mutu, ya ci gaba da bibiyarta. Kuma ta sa a ranta cewa ba za ta taba sake komawa su ci gaba da soyayya ba ko me zai yi a kanta saboda ta san cewa ba za ta aure shi ba,” in ji Rabi’a.
Yadda aka kashe matashiyar
Mahaifiyar Ummita, matashiyar nan da saurayinta dan kasar China ya yi wa kisan gilla a Kano, ta ce a gabanta abin ya faru.
A bayaninta bayan jana’izar Ummita da aka gudanar a safiyar ranar Asabar, mahaifiyar ta ce, dan Chinan ya ritsa ’yar ne a daki ya rika daba mata wuka.
Ta ce, “’Ya ta ce, yana yawan zuwa wurinta, amma tana kin kula shi.
“Da ya zo wannan karon sai ya yi ta kwankwasa kofa, da na ji yadda yake dukan kofar da karfi ya ishe ni sai na je na bude.
“Ina budewa sai ya ture ni gefe ya shiga cikin gidan ya fara caccaka mata wuka.
“Shi ne na yi ta kururuwa mutane suka shigo a guje, muka garzaya da ita zuwa asibiti, amma kafin mu isa rai ya yi halinsa.
“Abin ya faru ne da misalin karfe 9.30 na dare,” ranar Juma’a.
“Ni da ita da kannenta mata biyu ne a gidan a lokacin; dan uwanta ba ya nan, mahaifinta kuma ya rasu.
“A lokacin ana ruwan sama, mutane sun shige gidajensu, ba za su iya jin ihuna ba, sai da wani ya zo ya shigo ta taga.
”Ina rokon da dauki mataki kan wannan abin da aka yi wa ’yata.
Tsohuwar budurwarsa ce
Ta ci gaba da cewa marigayiyar, “Sun taba yin soyayya, amma ta yi aure, daga baya auren ya mutu.
“Bayan rabuwar aurenta ne ya sake dawowa, ya matsa cewa yana son ganin ta.
“Yakan shigo, duk da cewa ba ma son hakan, amma shi bai fahimta ba; Wani lokaci har korar sa muke yi.
“Da na ce zan yi karar sa wurin ’yan sanda sai ’ya’yana suka hana, suka ce ba sai an fitar da abin da ke faruwa duniya ta sani ba.”
Yadda aka kawo dauki
Ta ce, “Mutumin da ya kawo mata dauki ta taga ya shigo gidan, kuma shi ne ya kama shi ya fito da shi waje.
“Har ya tsere, amma suka bi shi suka kamo shi suka dawo da shi yanzu yana hannun ’yan sanda.
“Ita ce babbar ’yata mace, amma akwai maza biyu kafin ita.
Abin da ya sa ya kashe ta
“Ya fahimci ba ta son shi, idan ya kira waya ba ta amsawa, shi ya sa ya yanke shawarar harin da ya kawo.
“Ya kusa awa daya yana buga kofar, ita ce ta nemi in je in sallame shi, amma da na bude kofar shiga gidan ya ture ni ya shigo gidan.
“Kai-tsaye ya wuce zuwa dakinta, domin ya san dakinta, saboda yakan shigo gidan; yawanci ’yan uwanta maza ke tisa keyarsa daga gidan.
“A Shoprite suka fara haduwa lokacin da ta je sayen turare inda suka karbi lambar juna, daga baya suka fara waya.
“Da ta yi aure sai suka rabu. Har mijinta na zargin cewa suna chatting da shi; amma ba wannan ne sandaniyyar rabuwar auren ba.
“Tabbas ta fada mishi cewa za ta aure shi, amma da ’yan uwan mahaifinta maza suka ga wasu matsaloli sai suka ki amincewa, kuma na goyi bayan dalilansu,” in ji ta.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce sai daga baya zai fitar da karin bayanai.