Shugabannin ’yan bindiga a Jihar Zamfara, ciki har da dan Buharin Daji, tsohon shugaban ’yan bindiga da aka kashe na shirin mika wuya ga Gwamnatin Jihar.
Gwamnan Jihar Zamfanra, Bello Mohammed Matawalle, ya ce an kammala tattaunawa da Dan Buharin Daji da mahaifiyarsa da wani babban jagoran ’yan bindiga kan su ajiye makamansu.
- Abduljabbar: Kotu ta ba da izinin hana shi wa’azi da rufe masallacinsa
- An girke jami’an tsaro a gidan Sheikh Abduljabbar
- Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar kan ‘batanci ga Sahabbai’
- Raddin Sheik Abduljabbar ga Ganduje
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin fitaccen malamin Musulunci da ke shiga kauyukan Fulani yana musu wa’azi kan zaman lafiya, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi wanda ya je jihar Zamfara domin tattaunawa da shugabannin ’yan bindiga a kan su ajiye makamanasu.
Gwamnan ya bayyana wa Sheikh Ahmad Gumi cewa shawarar da shugabannin na ’yan bindigar ya yanke na daina ta’addanci zai taimaka wajen samun zaman lafiya ta hanyar tattaunawar da gwamnatin jihar take yi da ’yan bindiga a Jihar.
“Da ban yi tsayin daka ba, da tuni na dakatar da sulhu da ’yan bindiga saboda irin matsin lambar da marasa goyon bayan tsarin suke yi min.
“Na ga bi-ta-da-kulli iri-iri saboda sulhun da nake yi da ’yan bindiga, wasu na zargi ina goyon bayansu, wasu kuma su ce ai ni daya ne daga cikinsu. Amma mun ga ribar sulhun tunda yanzu kasuwannin kauye sun fara ci.
“Mun kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa su ba tare harba ko da harsashi daya ba; Da mun san cewa karfi zai yi maganin matsalar da babu abin da zai sa mu yi sulhu.
“Za mu ci gaba da yin abin da muke ganin shi ne mafi a’ala ga jama’armu ba tare da la’akari da abin da wasu za su ce ba,” inji Matawalle.