✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Arewa ne kadai zai iya lashe wa PDP zabe a 2023 – Dokpesi

Ya ce ba yadda za a yi PDP ta lashe zaben in ta tsayar da dan takara daga Kudu.

Wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Cif Raymond Dokpesi ya ce jam’iyyarsa na da damar kwace shugabancin kasa daga APC a 2023 idan ta tsayar da dan Arewa takara.

PDP dai ta mulki Najeriya na tsawon shekara 16, kafin daga APC ta karbe mulki daga hannunta a 2015.

Sai dai yayin da zabukan 2023 ke kara matsowa, wasu na ta kiraye-kirayen ganin an mayar da mulki zuwa Kudancin kasar nan.

To sai a yayin wata tattaunawarsa da Daily Independent, Dokpesi ya ce wadanda ke hankoron a mayar da takarar jam’iyyar zuwa Kudu a 2023 na kokarin kwaikwayon APC ne kawai.

A cewarsa, ba yadda za a yi PDP ta lashe zaben in ta tsayar da dan takara daga Kudancin kasar nan.

Ya ce, “Dukkanmu ’yan Najeriya ne, saboda haka babu amfanin mu ci gaba da yaudarar kanmu a wannan lokacin. A matsayina na mai shekara 70, da kuma tarin ilimina wajen shirya yakin neman zabe, ina mai tabbatar maka a ra’ayina, matukar ba mu tsayar da dan Arewa takara ba, to ba shakka ba zamu kai labari ba.

“Batun cewa a mayar da mulki Kudu bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu, wannan yunkurin kwaikwayon tsarin APC ne.

“Amma mu a PDP, ya kamata mu tsaya mu fada wa kanmu gaskiya. Olusegun Obasanjo daga Kudu maso Yamma ya yi shekara takwas, Goodluck Jonathan daga Kudu maso Kudu ya yi shekara shida, jimlar shekara 14 kenan.

“A bangare daya kuma, Umaru ’Yar’aduwa daga Arewa ya yi shekara uku, ka ga kenan akwai banbancin shekara 11. Da a ce ba a yi wa Atiku Abubakar magudi a 2019 ba, da sai ya dawo ya nemi wa’adi na biyu a 2023. Akwai wanda zai ce hana shi? Babu!

“Saboda haka, a PDP, ya zama wajibi dan takararmu ya fito daga Arewa. Mutane su kara hakuri saboda dole mulki zai kara dawowa Kudu a nan gaba,” inji shi.

Dangane da fafutukar da ’yan kabilar Ibo suke yi na samar da Shugaban Kasa a zabe mai zuwa, Dokpesi ya ce ko da yake yin hakan tabbatar da adalci ne ga yankin Kudu maso Gabas, kasancewar shi kadai ne bai samar da Shugaban Kasa ba daga Kudu tun shekarar 1999, ya ce ko da an basu takarar ba za su iya lashe wa jam’iyyar zabe ba a wannan lokacin.