An bayyana cewa damka jan ragamar kasar nan a hannun matasa ne kadai abin da zi kai kasar ga gaci. Wannan bayani ya fito ne daga Aminu Abdurrahman Malesh wanda shi ne Shugaban kungiyar Council of Young Leaders of Nigeria, kungiyar da ke fatufutuka kan harkokin siyasar kasar nan.
Alhaji Aminu Malesh ya bayyana cewa matukar ana so a samu gyara a tsarin tafiyar da mulkin Najeriya to dole sai an kawar da tsofaffin jini daga harkar mulkin kasar nan “Tun da muka taso mulkin kasar nan yake jujjjuyawa a hannun tsofaffin mutane. Wadanda suke mulkin nan tun shekaran jiya, kuma su ne dai ke yi har yanzu babu canji. Idan mun lura su suna neman mulkin ne ba don talakawa ba sai don wata manufa.
Wani dan siyasa ya bata masa shi ma idan ya hau mulki zai rama. Muna so mu sami mutumin da yake ba shi da wani kulli tsakaninsa da wani wanda kishin kasar ne a gabansa. Wannan ba kowa ba ne sai matashi wanda idan ya hau zai gyara harkar ilimi tare da samar wa matasa aikin yi.
Shugaban matasan ya bayyana cewa tsawon shekaru uku da aka sami wannan gwamnatin matasan kasar nan ba su san ana gwamnati ba, duk kuwa da cewar da bazar matasan ake rawa amma da zarar sun gama tura motar sai a bar su da hayaki “Gaskiya duk wanda yake duba yadda abubuwa suke tafiya a wannan gwamnati, to babu wanda zai ce matasan kasar nan sun samu wani ci gaba. Babu abin da matashi yake bukata a rayuwarsa kamar ili da kuma sana’a. idan har yana da wadanan abubuwa ba shi ba bangar siyasa. Amma sai gashi gwamnati ta gaza smaarwa matasa wadanann abubuwa. Abin takaici ne kason da aka ba harkar ilimi a kasafin kudin bana. Haka kuma batu aikin yi matasan kasar nan ba su gani a kasa ba.
An ce za a sama wa mutum miliyan biyu aikin yi amma har yanzu daga labaran da nake samu a wajen shugabannin matasa na garuruwa daban-daban, ba a samu mutum miliyan daya sun amfana ba. Ko harkar aikin N-Power da ake takama an samar matasa bas u amfana sosai ba yawancin ma aikatan gwamnati ne suka amfana. Ya bayyana cewa matukar ana so matasa su daina bangar siyasa to sai an ba su ilimi tare da sama musu aikin yi.”
Shugaban matasan ya yi kira ga ‘yan uwansa matasa da su daina yarda yan siyasa suna amfani da su wajen cimma wasu bukatunsu, a maimakon haka su mayar da hankali wajen tunanin makoma mai kayu a garesu. “A duk lokacin da aka zo yin zabe kada wani ya zo ya sa mu mu shiga bangar siyasa.
Duk wani shugaba da yake bayar da makami to kafin mu karba. mu fara ganin dansa a gaba mu kuma matasa sai mu ce wallahi yaki sai inda karfinmu ya kare. Amma inde dan siyasa zai dauke dansa ya kai kasar waje karatu sannan ya ba mu makami mu yi banga to mu nuna masa mun ki wayon. Ina so na kara kira ga matasa mu hada kanmu ya zamto muna da hukunci akan kanmu idan muka zabi mutum bai yi mana komai ba to mu yi masa kiranye mu sutale shi.
Sannan abu na gaba matasa su fito su yi siyasa su nemi tnuna wa duniya cewa za su iya. Muna so a wannan karon 2019 matasa su futo su gwada domin samin sauyi”.