✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Damisa da Dila

Barka da warhaka Manyan Gobe, da fatan an shiga sabuwar shekarar 2019 lafiya.  Sannan da fatan an shirye-shiryen komawa makaranta bayan an sha hutu.Yau filin…

Barka da warhaka Manyan Gobe, da fatan an shiga sabuwar shekarar 2019 lafiya.  Sannan da fatan an shirye-shiryen komawa makaranta bayan an sha hutu.Yau filin naku yana dauke da wani gajeren labari ne wanda ke kunshe da darasi mai amfani ga rayuwarku. A sha karatu lafiya.

 

“Idan baki ya san abin da zai fada bai san abin da za a mayar masa ba.”

Akwai lokacin da dila da damisa suka yi makwabtaka da juna har ya zamo cewa idan sun dawo daga farauta sukan zauna su yi hira.

Wata rana sai damisa ya kalli jikinsa sannan ya kalli na dila sai ya fara yabon irin kirar halittarsa yayin da ya rika kushe kirar halittar dila.   Dila ya fakaici idon damisa ya yi gatsine sannan ya sanar da shi idan ya fi ta kyaun fata ai bai fi ta wayo ba. Dila ya tuna wa damisa irin wautar da ya yi a lokacin da kafarsa daya ta makale a cikin wani rami, maimakon ya janyo kafar da ta makale a hankali sai rashin dabara ya sa ya sake jefa daya kafar da niyyar ya zaro su biyu a tare da hakan ya sa duka biyun suka makale.

Ana cikin haka ne dila ya samu damisa a haka daga nan ne ya yi dabara ya kubutar da daminsa daga hallaka.

Nan da nan damisa ya raina kansa da ya ji wannan kalami, don ya san gaskiya ne. Daga nan ya harzuka inda ya kai wa dila hari amma saboda wayo irin na dila sai ya gudu ba tare da damisa ya kama shi ba.

Daga nan ne dila ya shaida masa cewa “In baki ya furta magana ba san irin amsar da za a mayar masa ba”.

Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a wannan labari.