✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee

Ta ce Musulmi na mata dariya suna zagin ta, Kiristoci kuma na tausaya mata bayan an damfare ta N450m

Tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zee-zee ta bayyana cewa wasu sun nuna mata kauna a lokacin da ta yi yunkurin kashe kanta, amma kuma a cewarta wasu abin dariya ma suka dauke ta.

Ummi ta kara da cewa ta yi takaicin yadda wadanda ba addininta daya da su ba suke ta mata jaje, amma ’yan uwanta Musulmi suka rika zaginta suna mata dariya.

A cewarta, “Ba zagi na da aka yi ba ne ya ba ni haushi ba, abin da ya ban haushi shi ne a ce ina Musulma kaddara ta same ni, amma sai wadanda addininmu ba daya ba su ne za su nuna alhininsu a kan damfara ta da aka yi? Sai yanzu na fahimci arnan Najeriya wallahi sun fi Musulman Najeriya tausayi. Don haka Allah wadaran Musulmi masu irin wannan mummunar zuciyar.”

Idan ba a manta ba, a makon jiya ne Ummi Zee-zee ta yi yunkurin kashe kanta saboda damfarar ta da aka yi na kudi Naira miliyan 450.

Sai dai ta kara da cewa abubuwa uku ne suka sa ta yi yunkurin, inda ta ce, “Tabbas na so na kashe kaina din domin abubuwa guda uku da suke damuna. Na farko mutuwar babana, na biyu ina son wani namiji da ya mutu, sai na uku damfarar da aka min.”

A karshe Ummi ta ce tuni wasu masu gidanta suka fara tura kudade domin rage mata radadin asarar.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by ummi ibrahim zeezee (@ummizeezee)