✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambarwar damben dandatsar damatsa

Dandatsar damatsa Dararrakun dartsa Dudugar dusa Darkakin dasisa Dundumin nunin yatsa   Masu kamun kifi da fatsa Azargagiya an watsa Ruwa ya fallatsa Kwaramniyar kwankwatsa…

Dandatsar damatsa

Dararrakun dartsa

Dudugar dusa

Darkakin dasisa

Dundumin nunin yatsa

 

Masu kamun kifi da fatsa

Azargagiya an watsa

Ruwa ya fallatsa

Kwaramniyar kwankwatsa

Watsattsaken tafiyar tsutsa

 

Kowa ya ji matsa

Karfa-karfa aka kitsa

Kulle-kullen dakin da aka kutsa

Wawaye aka latsa

Haurobiyawa a motsa

 

Ka da dai a yamutsa

Kowane bangare a kimtsa

Hutsun hautsinin hargitsa hantsa

Rotse-rotse sun so su ratsa

Rangajin raruma ya runtsa

 

Na-mujiya a cire kwantsa

Kar dai ai kwarankwatsa

Ko ai uwar watsi watsa-watsa

Gudumar gungunin gundumar gwamutsa

Tsirin tsitaka mai tsatsa

 

Ruguntsimin rungumar rigima

Rugugin rarakar rikon ragama

Raka-rakar rokar Rasha a sama

Rummace ne dai na rama

Ragamar rikon rakuma

 

Rudanin rashin kunya

Rawar dibar kanya

Rarumar kayan jama’a

Rahoto ne ta cikin samma’a

Reshen jar-miya ruwaya-ruwaya

 

Hukumar zabi-sonka

Ki warware kiki-kaka

Dawurwurin badakala

Ta haifar da lalala

A shawo kan turka-turka

 

A duba kundin doka

Kar a bari kowa ya koka

Jama’a komai na da ka’ida

Sai an bi a samu fa’ida

Sai a ji dadin harka

 

Makon da hukumar zabi-sonka ta kasa ta ayyana karkare zabukan da ke ta zababbaka, al’amura sun yi kiki-kaka, don haka babu KAMMALALLEN ZABI-SONKA, shi ya sa aka ware wata rana don karkare zabukan da ake tuhumar kimar ingancin alkaluman kuri’unsu; ta yiwu bisa dalilan DANNIYA DA MURDIYYA, HANDAMA DA BABARE, uwa-uba ARINGIZO. Sannan akwai matsalar KARTAR RADI, na’urar tantance ce-ce-ku-cen wane-ne, wace-ce ya/ta cancanci kada kuri’a.

Bisa la’akari al’amuran da ke wakana a sassan kasar nan, inda duk JAM’IYYA MAI DANBOTO DA SANDA JIRGE ke kan gaba a kidayar alkaluma nan ne aka samu tsaikon jimurdar KITIMURMURAR DAMBARWAR DAMBEN DAKATAR DA ZABI-SONKA. To ni dai a iya al’amuran da na fasko, jam’iyyar danboto ta kware da rinto, uwa-uba handama da babakere. Sai masu hankali a kwanyarsu su bi kadin al’amuran da suka wakana tun daga shekara ta alif sili da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa zuwa shekara ta dubu karamin lauje da sili da baban lauje: daga zamanin jan ragamar Haurobiya karkashin juyin akalar rakuman Baba-ojo mai gonakin Ottawa, zuwa kan Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki. Shin a tsawon wancan lokaci wace irin murdiyyar zabi-sonka ce ba yi wa al’ummar kasar nan ba?

Masana dai sun tabbatar da cewa babu wani KAMMALALLEN ZABI-SONKA, sai dai akwai KARBABBEN ZABI-SONKA, wai idan an murguda baki kamar ana cin kilishi, an kan ga gilashi ana yaren Ingilishi, sai kawai ku ji an furta cewa, “THERE IS NOTHING CALL PERFECT ELECTION BUT THERE IS CREDIBLE ELECTION.” Bisa wannan dalili lallai mu lalubo bakin zaren warware tsilli-tsillin matsalolin da ke tattare da harkar zabi-sonka a kasar Haurobiya. Kananan matsalolin da za a iya shawo kan su, sai a tarairaye su, ta yadda alkaluman zabi-sonka za su samu karbuwa, wadanda kuwa ba za a iya warware kitimurmurar da ke tattare da su ba, ya zama wajibi a sake sabuwar saka, ba tare da takun saka ba.

Lallai ina jan na-zomon masu fuka-fukin tashi, ka da wani mugun mai wasan SAMSON-SIYA-SIYA DA KWAKWALWAR TALAKAWA ya rika DUKAN TA-MOLA da juyin KARATUN WASIKAR JAKIN DAWA DA NA-GIDA  a tsakaninku, har ku ji cewa, in kun kawar da wane daga kan kujera tamkar kun yi fafutikar JUYIN JUYA HALIN BOLSHEBIK, wato sanadiyyar kawar da masu sarautun gargajiya da attajiran kasar Rasha; ko kuma ku dauka kun aiwatar juyin juya halin LOGAR LUGGAR LARABCIN LARABAWA, kamar yadda aka tsuwurwurta a wasu sassan Tsakiyar Gabashin Duniya. A dai kiyaye TUGGUN TAGIYYA ko TAMBELEN TUMBIN-WULLI, ko wata KWARAMNIYAR KWARANKWATSIN TSIWAR TSIYA-TSIYAR TSIRA TSITAKA MAI TSATSA A TSAKANKANIN AL’UMMA.

Haurobiyawa, ana ta yada kiren kanzon kurege kan cewa Baban-burin-huriyya ne ya bukataci Hukumar zabi-sonka ta kawo wa ’yan adawa tarnaki, don kar su kai ga gaci. Hakika wannan zuki-ta-malle ce kama-kolo-ka hada shi zomo. Da Baba na son aiwatar da mummunar manufa, tabbas da an wancakalar su DANNO MAI ALAYE da DAGIRGIRIN DOGARIN WAKILAN RAFKANUWAR RAFKE AL’UMMAR KASAR NAN.

’Yan makaranta ku sani ba duk batutuwa da aka baza a shafukan TUKIN-TUWON-TITI da FUSKANTAR-BOKOKO da WATSO-WATSON-ZUFFA suka tabbata a doron sukuwar ingarman karfen karafan titin tarragon kwangirin layin dogo ba; lallai mu kyautata alkiblar tunani ba tare da bata lokacin wulkitawar hanayen agogo ba. Lallai kamar yadda na sha bijiro da al’amura tare da kiraye-kiraye a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintaciyar jarida kasar Haurobiya sai mu yi karatun ta-natsu don kar mu karke da mutsu-mutsu. Hasalima dai Arewatawa ku ne ya kamata a ce kun warware wa kowane sashe na kasar nan dabarbarun TANTANCE TSAKANIN TSABA DA TSAKUWA.

Mu dai bi al’amura a hankali, a hankali, mu daina cin dunduniyar juna, kar mu karke da DANDATSAR DAMATSAN DUNDUMIN DARARRAKUN DARTSA; ko HUTSANCIN HAUTSININ HARGITSA HANTSAR HADIN HADAKAR KAN KASA.

Idan na-zomo ya ji, na-mujiya ya gani ba ya ki gani ba, to gangar jiki ta tsira. JIKI DAI MAGAYI BANKAR BUKIN DAN KORAU!