✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Dalilina na kashe matar dan uwana bayan na yi mata fyade’

Matashin nan mai shekaru 25 da ake zargi da kashe matar dan uwansa bayan ya yi mata fyade ya ce ya yi hakan ne don…

Matashin nan mai shekaru 25 da ake zargi da kashe matar dan uwansa bayan ya yi mata fyade ya ce ya yi hakan ne don ya huce haushin sabanin da ke tsakaninsa da wan nasa wanda suke ‘yan uba da shi.

A zantawar da jaridar Punch matashin ya ce ya yin hakan ne saboda dan uwan nasa ya kore shi daga wurin da yake masa aikin leburancin gini ne.

“Bayan ya sallame ni daga inda nake masa leburnci sai na koma ba ni aikin yi tun da dama san’ar ginin nake yi.

“Ba zan iya kashe dan uwan nawa ba saboda yafi karfina, ba zan iya tunkarar sa ba, don haka na huce fushina a kan matarsa na kashe ta.

“Ba na jin komai don na kashe ta, sai dai ina jiran hukunci. ‘Yan sanda sun harbe ni a kafa da suka zo kama ni”, inji shi, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Ta kara da cewa wanda ake zargin ya ce wansa yana Abuja a lokacin da ya aikata laifin a jihar Zamfara, kuma yana sauraren hukuncin da za a masa domin yana sane da cewa laifin ya yi mummuna ne.

A kwanakin baya rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta gabatar da Aminu Bala ga manema labarai wanda ake zargi da laifin kashe matar dan uwansa Hauwa Iliyasu bayan ya yi mata fyade.

%d bloggers like this: