✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na yi murabus a kocin kulob din Giwa – Koci Aminu

Aminu Musa shi ne tsohon kocin kulob din Giwa da ke garin Jos a Jihar Filato, a hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara…

Aminu Musa shi ne tsohon kocin kulob din Giwa da ke garin Jos a Jihar Filato, a hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara harkar kwallon kafa, matsalolin da ya fuskanta, nasarorin da ya cimma da kuma dalilin da ya sa ya yi murabus a kocin kulob din Giwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Bashir Liman, Jos

Za mu fara da gabatar da kanka?
Assalamu alaikum, sunana Aminu Musa, wanda aka fi sani da Aminu Gola.  An haife ni a ranar 1 ga Afrilu, 1969 a garin Jos, na yi karatu da kuma harkar kwalllon kafa a cikin garin Jos.
Me ya ja hankalinka har ka fara harkar kwallon kafa a Najeriya?
Tun ina makaranta ni mutum ne mai sha’awar kwallon kafa, daga farko ban damu da kwallo ba, amma da yake yayyuna duk sun buga kwallo, wani lokaci sukan kai ni don in yi kallo, to daga nan ne ta fara shiga raina, tun ina dauko musu kwallo, har wata rana idan golansu bai zo ba za su ce in kama musu gola, abin ya shige ni sosai har na fara kama gola ina aji uku a makarantar sakandare. Malaminmu a bangaren wasanni ya ce mini in bada hankali a kwallo domin zan ci abinci da ita.
Akwai wani kamar yaya yake a wurina, ya tara ’yan kwallo, shi ne kyaftin din kwallon kafa na Najeriya a lokacin Medico 1983, shi ma nakan bi kulob dinsa in kalli wasa, ana nan sai suka shiga gasar Trebor Cup a Bauchi, sai na bi su, golansu ya samu matsala, sai sauran ’yan wasa suka ce in kama musu gola, ni ne karami a cikinsu. Allah Ya ba ni iko na kama har zuwa wasan karshe. Mun cire su Manu Garba ne a wasan karshe.
Daga nan kulob na zama golan Mai Hala FC a lokacin suna buga gasar Super League dibision 4. 1987 sai ITF suka sayi kulob din, kuma daidai zan kammala sakandare ke nan. Na zama kyaftin din Plateau state academy. Daga nan Koci Sama’ila Mabo ya ce mini ga shi an kirkiro kulob din Mighty Jets da kuma Plateau United, ya kamata mu karfafa Mighty Jets, wato a 1990 ke nan. Daga 1990 zuwa 2003 ina tare da Mighty Jets. Na bar Jets a 2004, amma a shekarar suka sake kirana, inda muka ci kofin kalubale a shekarar. Duk kocin da na yi aiki da shi sai ya ce mini nan gaba zan zama wani abu, ni kuma na kwantar da hankalina ina koyon aikin koci a wurinsu.
Yaushe ka fara aikin kocin?
Babu wanda zan yi wa godiya kamar kocin Jihar Filato a lokacin wato Ben Dalong ke nan, sannan Sama’ila Mabo da Ajala, amma wanda ya saka ni a harkar kocin ya matsa mini har na samu takarda a kan kocin shi ne Ben Dalong. Bayan Mighty Jets sun fara buga firimiya a lokacin mun je Kwara wasa sai ya hada ni da marigayi Koci Yemi Tella. Sai na fara horar da gololi, na fara kocin gololi a shekarar 2004 a Mighty Jets. Na bar Jets a 2009. Daga nan muka kafa kulob din Kanu Foundation. A lokacin sai wani Bature darakta ne a kamfanin Adidas ya ga yadda nake aiki, sai ya ba ni wadansu takardu, ya ce idan na bi su sau da kafa zan yi nasara a bangaren kocin. Daga nan Sakataren harkokin kwallon kafa na Jihar filato Alhaji Yakubu Daniel ya gayyace ni don a bude kulob din Giwa FC. Ya ce mini Chris Giwa zai bude kulob, da ma shi Giwa din mun yi aiki da shi a Mighty Jets, a lokacin ina mataimakin kyaftin. Bayan na ba su takarduna ne sai suka dauke ni a matsayin mai horar da gololi.
Shekarar farko muka zo na biyu na rukunin dibision 2 ke nan, shekara ta biyu muka hauro Firimiya. Daga nan aka fara fafatawa, ka san maigidan namu mutum ne mai son a samu nasara a wasanni, mun samu rashin nasara a wadansu wasanni, sai ya sauke kowa, bayan mun tafi gida sai aka ce an dawo da ni, sai ya tambaye ni zan iya rike kulob din, na ce masa zan iya, domin na san yaran kasancewar da ni a aka hada su. Ya ce to jibi yana da wasa a Fatakwal in kai kulob din. Na kai yaran muka samo maki daya, muka je Taraba muka samo maki uku, sai da muka buga wasa 9 ina samun nasara.
Daga nan ya kawo Kadiri Ikhana, shi kuma ya ce ya zo ya taya ni aiki, ba wai ya kwace mini kulob ba, muka yi aiki da shi bayan wata daya ya bata da maigidanmu. Na karbi kulob din yana matsayi na 11, sai da na dawo da shi na 4. Daga nan ya ce ya bar mini kulob din in sake hada masa ’yan wasa. Ana nan na hada kulob, a wasan farko aka ci mu 3 da ba ko daya, sannan muka yi kunnen doki a gida, sai ya ce mataimakina ya ci gaba, ni kuma in koma karkashinsa, ko a lokacin na samu kulob-kulob da suke so na, amma na fi son in daukaka darajar Giwa a duniya. Na koma kasa, sannan muka ci gaba da aiki. Daga nan muka yi wasa 8 ba a samu nasara a kanmu ba. Daga baya ya sake dawo da nauyin kaina, sannan aka mayar da mu Kaduna, Allah Ya taimake ni na samu nasara a wasannin da muka buga a Kaduna. Ya sake dawo da abokina. Bayan an ci mu kwallaye 4 a Sunshine ne sai ya ce kowa ya sauka, daga nan ya sake dawo da ni. Daga nan na samu nasara a kan Enyimba.
Me ya sa ka ajiye aikinka a matsayin kocin Giwa FC?
Maigidanmu mutum ne da yake ajiye ’yan wasansa a wuri daya, ba ya so su rika yawo. Na zauna da Chris Giwa shekara 4, na bi shi inda yake so, bara ina aikin nan mahaifiyata ta rasu, amma ban samu damar an yi jana’izarta da ni ba, a wannan karon sai kishiyarta ba ta da lafiya, a dakinta na taso. Na kira shi a waya don in sanar da shi halin da ake ciki amma ya ki daukar wayata, a lokacin muna kan hanyar dawowa daga Taraba, inda a can aka ci mu daya da babu, na ce sakatarensa ya sanar da shi halin da nake ciki, na ce to idan ya bugo waya ya sanar da shi a matsayina na koci zan je in ga mahaifiyata, domin idan ta farfado sunana take kira.
Na ce tun da babu atisaye a ranar, to zan je in ganta, sai na tafi, washegari sai sakataren ya ce wai oga ya ce an dakatar da ni. Ita ce ta daure mini gindi nake harkar kwallo, domin mahaifiyata ba ta so. Daga nan ne sai ni da manajojina muka yanke shawarar in ajiye aikin.
Mene ne burinka a harkar kwallon kafa?
Burina ina zama babban koci a duniya, in rika samar da ’yan wasan da za a rika alfahari da su.
Wadanne matsaloli ne kake ganin suke ci wa harkar kwallon kafa a Najeriya tuwo a kwarya?
Matsala ta farko na dora ta a kan ’yan wasa, akwai ’yan wasa a Najeriya amma suna sauri, kowace unguwa ka je za ka samu ’yan kwallo, amma ba sa tsayawa su koyi kwallon yadda ta kamata, sannan wadansu iyayen sukan hana ’ya’yansu mayar da hankali. Ta bangaren koci-koci kuma wani lokacin suna nuna son kai, ko son zuciya, ko kin yin aiki tsakani da Allah. Sai ta bangaren jami’an da ke lura da harkar kwallo a Najeriya (LMC), idan an ba su hakkinsu to su ma su sauke nauyin da ya rataya a kansu, idan an ba su amana, to su rike ta. Ya kamata jami’ai su rika lura da yadda ake harkar kwantiragin koci-koci a Najeriya, ina kalubalantarsu idan ka cire kwantiragin manyan-manyan koci a Najeriya, to LMC ba ta da takarda ko daya da ke dauke da bayanan koci a Najeriya.
Wadanne nasarori kake ganin an cim ma a harkar kwallon kafa zuwa yanzu?
Duk da cewa akwai matsaloli har yanzu amma jami’an LMC sun yi kokari, sun cire mana cutar cewa kowa sai ya samu nasara a gidansa, ana cin kowa a gida. Alkalan wasa suna kokari. Sannan yadda ake biyan ’yan wasa ya canza, da ba a biya sosai, yanzu kuwa za ka ga dan wasa cikin walwala da kwanciyar hankali. A da ba a nuna wasanni a gidajen talabijin kamar su Super Sport, amma a yanzu al’amarin ya canza.
Yaya kake ganin harkar kwallon kafa a nan gaba?
Lokaci zai zo da harkar kwallon kafa a Najeriya za ta bunkasa har a rika bada misali da ita a duniya, idan ka lura a yanzu an fi cika a filayen wasa idan ka kwatanta da shekarun baya.