Mawallafin jaridar nan na Kaduna, Tukur Mamu, ya bayyana dalilin da ya sa ya janye daga shiga tsakani don a sako fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Dan jaridar, wanda kuma jami’in tuntuba game da sha’anin yada labarai ga Sheikh Ahmad Gumi, ya ta’allaka rashin goyon baya daga bangaren gwamnati a matsayin daya daga cikin dalilan da suka sa shi ya janye.
- Tsohon Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Tafa Balogun, ya rasu
- Dalibin SS 1 ya rataye kansa saboda faduwa jarrabawa
Mamu, wanda shi ne mawallafin Jaridar Desert Herald, ya taka rawar gani wajen kubutar da 11 daga cikin fasinjojin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a watan Maris din da ya gabata.
Haka nan, ya taimaka wajen sako karin mutum bakwai a Yulin da ya gabata.
Da ake tattaunawa da shi a cikin shirin da tashar Arise TV ta yi da shi a ranar Alhamis, Mamu ya ce gwamnati ba ta nuna wata alamar mara masa baya ba wajen tattaunawa da ’yan bindigar kan yadda za a kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su din.
Ya ce, “Na sanar da janyewata daga shiga tattaunawa da ’yan bindigar saboda ina da dalilaina. Na daya, idan kana wani abu kai kadai, ko da ka yi nasara a kan haka, nasarar za ta kasance kadan ce.
“Sannan a yanayin da ya zamana babu wani goyon baya daga bangaren gwamnati, babu nuna godiya, hasali ma sai kokarin barazana ake yi maka.
“Ba na zargin kowa, kuma ba na zargin hukumomin tsaro. Amma a gaskiya abin da na gani da kuma wahalar da na sha, musamman da rashin goyon baya daga gwamnati, zai zamana da hatsarin gaske na ci gaba da haka.”
Dan jaridar ya kuma ce, yana tsoron kada ya rasa ransa wajen tattaunawar, kuma ya janye ne saboda har yanzu gwamnati ba ta fahimci girman matsalar ba.
“Mutum na iya fuskantar hatsarin rasa ransa, ba wai ta dalilin ’yan bindigar ba, amma ta dalilin gurbatacciyar al’umma.
“Saboda haka, duk yadda ka kai da son taimakawa, muddin babu hadin kai daga bangaren gwamnati, musamman kuma a mawuyacin hali irin wannan, ina ganin mafi kyawun mataki shi ne ka tsame hannunka. Watakila har sai lokacin da gwamnatin ta fahimci girman matsalar tukuna,” inji shi.