✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa aka hade hukumar wasanni da ma’aikatar wasanni wuri daya

Ma’aikatar wasanni ta kasa ta bayyana dalilin da ya sa ta hade hukumar kula da wasanni (NSC) da kuma ma’aikatar wasanni. Ministan ma’aikatar wasanni ta kasa…

Ma’aikatar wasanni ta kasa ta bayyana dalilin da ya sa ta hade hukumar kula da wasanni (NSC) da kuma ma’aikatar wasanni.
 Ministan ma’aikatar wasanni ta kasa Barista Solomon Dalung ne ya bayyana dalilan rushe hukumar ta wasanni da hade ta da ma’aikatar wasanni ta kasa a lokacin da yake jawabi.  Ya ce babban dalilin shi ne babu dokar da ta nuna a kafa hukumar wasanni ta kasa a kundin tsarin mulkin kasar nan.
 Barista Solomon Dalung ya fadi haka ne yayin da mukaddashin shugaban hukumar sayar da hannun-jari ta kasa watau (BPE), Dokta bincent Onome Akpotaire da manyan ma’aikatan ma’aikatar suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Abuja.  Ya  ce wannan gwamnati ta yi tsayin-daka don inganta harkokin wasanni.
 A takardar sanarwa da jami’in watsa labarai na hukumar ta BPE Mista Aled Okoh ya sanya wa hannu ta nuna Ministan ya ce, ana bukatar ’yan kasuwa da su jajirce domin kanbama wasanni don rage yawan matasa masu zaman kashe wando da kuma burin ganin an  hana su aikata laifi.
 A jawabinsa, mukaddashin shugaban hukumar Dokta bincent Onome Akpotaire ya shaidawa Ministan cewa, don magance rashin kula da filayen wasanni mallakar gwamnati a kasar nan akwai bukatar a mika su ga kamfanoni masu zaman kansu don ganin sun cigaba da kula da su ba tare da an samu matsala ba.  Ya ce hakan ta sa ake da burin mika filin wasa na Surulere da ke Legas da kuma filin wasan Abuja ga kamfanoni masu8 zaman kansu don su cigaba da kula da su.  Sai dai ya ce har yanzu gwamnati ba ta yanke shawarar yin hakan ba, amma yana fatan Ministan zai gabatar da wannan kuduri ga gwamnatin tarayya don a amince da hakan.