✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa adabin Arewa ke bukatar cikakkiyar kulawa – Shugaban NOUN

Shugaban Budaddiyar Jami’ar kasa ta Najeriya (NNOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu ya ce babban taron shekara-shekara da ke mayuar da hankali wajen nazarin  Adabi a…

Shugaban Budaddiyar Jami’ar kasa ta Najeriya (NNOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu ya ce babban taron shekara-shekara da ke mayuar da hankali wajen nazarin  Adabi a Arewacin Najeriya ya cancaknci cikakkiyar kulawa da mayar da hankali tare da kima ta musamman dauke da tarihi.

Shugaban Jami’ar ya fadi hakan ne a daidai lokacin da yake gabatar da jawabin maraba a wajen taron adabin Arewacin Najeriya na shekara-shekara karo na 11, wanda jami’ar ta dauki nauyin gudanarwa a hedkwatarta da ke Abuja.

Ya ce taron wanda ya tatttaro mahalartansa daga ciki da wajen kasar nan, an tsara shi ne yadda zai jawo hankalin kan dimbin adabi mai cike da tarihi a yankin ba tare da la’akari da addini ba..

Adamu, wanda ya kasance mai masaukin baki a wajen taron, ya ce taron na shekara-shekara ana daukar nauyin gudanar da shi ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Jihar Kwara, inda a yanzu ya zama na jami’o’i uku, sakamakon shigowar jami’ar NOUN a jerin  masu daukar nauyin gudanarwar.

A cewarsa, taron an shirya shi ne don “ bunkasa sha’awar nazarin al’adun gida a wannan yanki a daukacin fannonin ilimi.”

Kasancewar Musulunci ya fara shigowa yankin tuna a karni na 11, Adamu ya ce, “yankin ya samu yaduwar ilimin addinin Musulunci da Larabci wadanda suka kafu sosai a harkokin koyarwa a makarantun Alkur’ani ga kowa, wato matasa da tsofaffi, maza da mata ba tare da la’akari da matsayinsu a cikin al’umma ba, al’amarin da ya ci gaba har zuwa lokacin da mulkin mallaka ya dan dakatar da al’amuran bayan da Birtaniya ta ci kasar da yaki a shekarar 1903.

Ya yi bayanin matakan bunkasar adabi a yankin, musamman abin da ya kira “zamanin kasurar rubataccen kagaggen labari a tsakanin al’ummar yankin. Farfesa Graham Furniss na Makarantar Nazarin Al’adun Asiya da Afirka, wanda a halin yanzu yake tare da mu, ya yi kyakkyawan aiki wajen tattara bayanai da alkinta adabi a mujallun da ake wallafawa da shafukan intanet, inda aka tara dimbin rubuce-rubuce.”

Daga bisani ya yi kira ga wadanda suka shirya taron da su yi la’akari da sauyin salon taken taron zuwa “Adabin gida a Najeriya,” ta yadda za a shigo da kowa da kowa da bunkasa al’amura.