✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Shugaban NNPP na Kasa ya yi murabus

Na kuma gamsu cewa wannan sauyi dole ya fara ta kaina.

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kasa, Farfesa Rufa’i Alkali, ya bayyana dalilinsa na ajiye mukaminsa makonni bayan Babban Zabe na 2023.

Wannan na kunshe cikin wata wasika da ya aike wa Sakataren Jam’iyyar na Kasa, kuma ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Farfesa Alkali ya ce ya ajiye mukamin nasa ne don bai wa sabbin jini dama, ta yadda za su dora a kan ci gaban da jam’iyyar ta samu cikin dan takaitaccen lokacin da ya yi yana jagorantar ta.

Alkali ya ce la’akari da irin abubuwan da suka faru kafin zabukan da suka gabata, da kuma a lokacin zabukan, yana cike da fatan cewa jam’iyyar adawar, na da makoma mai kyau.

Kuma a cewarsa, yana cike da fatan NNPP za ta kasance cikin manyan jam’iyyun siyasar kasar, da za su iya cin zaben shugaban kasa da sauran mukamai a kakar zabe ta 2027.

Ya ƙara da cewa don cimma wannan buri, NNPP na bukatar yin tunani da kuma kyakkyawan shiri, abubuwan da yanzu ne lokaci mafi dacewa na yin su.

Farfesa Rufa’i Alkali ya kuma ce jam’iyyar na bukatar sauye-sauye da dama, ta fuskar shugabancinta a matakai daban-daban domin kara karfafa matsayinta.

“Na kuma gamsu cewa wannan sauyi dole ya fara ta kaina. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ajiye mukamina, don ba da dama ga sabbin hannu su dora daga inda muka tsaya game da gudunmawar da muka bai wa NNPP,” in ji Alkali.

Ya kuma mika sakon godiya ga jagoran jam’iyyar na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da daukacin mambobin kwamitin amintattu na NNPP, da sauran zababbun ’yan siyasa na jam’iyyar bisa damar da ya ce sun ba shi wajen gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali.