✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da nake goyon bayan takarar Tinubu —Sanatan PDP 

Sanatan ya ce Tinubu ne ya fi dacewar ya goya ea baya a zaben 2023 duk da cewar a PDP ya ke.

Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani ya bayyana dalilinsa na goyon bayan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, duk da kasancewar shi dan PDP.

Nnamani, wanda Sanatan PDP ne mai ci yanzu, dama jam’iyyarsa ta dakatar da shi bisa zargin yi mata zagon kasa.

Dan majalisar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce bayan kasancewar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa na PDP, ya ce APC ta zo da tsari na bai wa Kudancin kasar nan damar tsayar da dan takarar Shugaban Kasa.

A cewarsa, kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadi cewa a rika karba-karba na manyan mukamai na siyasa tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da daidaito, adalci da gaskiya.

Sanata Nnamani, ya ce abin da PDP ta yi na kin mika takara ga Kudu, rashin adalci ne.

Tsohon Gwamnan ya kuma ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bisa la’akari da yadda tsarin kasar nan ke tafiya a tsakanin Arewa da Kudu, ya samar da daidaito inda ya bai wa Ahmed Bola Tinubu damar fitowa takarar Shugaban Kasa.

Ya ce, “Bayan na yi nazari sosai kan lamarin, sai na fuskanci cewar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya fi cancanta na mara wa baya a zaben 2023.”

Nnamani, ya ce akwai bukatar hadin kai a siyasance ta hanyar da za a bai wa dukkan sassan Najeriya dama.