✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin da na ƙona minija da man gyada’

Favour Nweke, matar da ta kona mijinta da tafasasshen man gyada a yayin da yake tsaka ta ce ta yi masa danyen aikin ne saboda…

Favour Nweke, matar da ta kona mijinta da tafasasshen man gyada a yayin da yake tsaka ta ce ta yi masa danyen aikin ne saboda rashin gaskiyarsa a zamansu da ita.

Uwargida Nweke ta fede biri har wutsi a yayin da aka gabatar da ita tare da wasu da ake zargi da aikata miyagun laifuka a harabar ofishin ’yan sanda a Jihar Ribas.

Ta ce “Na kona mijina ne saboda rashin gaskiyarsa; a kullum yakan fita da tsakar dare misalin karfe biyu ba ya dawowa gida sai da sassafe.”

Ta ci gaba da cewa duk lokacin da ta nemi ta ji ina yake zuwa da tsakar dare ya dawo gida da sassafe sai ya nuna mata ba abin da ya shafe ta ba ne.

Ta ce wata rana wani abokinsa ya kira ta a waya cewa “shin kina sane da halin da mijinki yake ciki? Sai na ce masa a’a.

“Ya ce da ni ga mijinki da wasu mutane rana ta baci musu, an kama su kan zargin wata badakalar kudi ta Naira miliyan 20 da suka shirya da wasu abokansa da suka zo daga Abuja,” in ji ta.

Ita kuma sai ta gaya wa abokin cewa “ni babu abin da ya gaya min sai dai kurum ya ce min yana shirin fita kasar waje; Haba gaskiya mana na ga dabi’unsa sun canja.

“Na san ya ce yana shirin fita kasar waje amma ba ni da wata msaniya” abin da ta gaya wa ’yan sandan ke nan.

Aminiya ta samu labari daga mazauna kauyen Ekehi da ke Karamar Hukumar Etche a Jihar Ribas, cewa bayan da matar ta kona mijin nata sai ta tsere, daga baya ’yan sintiri suka gano inda take a boye suka mika ta ga ’yan sanda.

Kakakin ’yan sandan jihar, Grace Iringe -Koko ta shaida wa wakilinmu cewa rundunar na tsare da wata mata a karamar hukumar Eleme kan zargin watsa wa mijinta sinadarin guba a fuska ta gudu ta boye.

Ta ce matar wacce  wacce ke da ’ya’ya biyu da mijin nata ta watsa masa sinadarin guba a fuska ne saboda an kawo kudin jangali da kamfuna ke bayarwa ana raba wa iyalai a kauyukan yankin.

Ita kuma mijin nata, da ya karbi kasonsu na kuɗin Naira dubu 15, maimakon ya kawo a kasafta sai ya hana.

Kakakin rundunar ’yan sandan ta ci gaba da cewa bayan mata ta yi wa mijin nata aika-aikan sai ta dauke katinsa na cirar kudi ta gudu da shi, ’yan sintirim  yankin ne suka kamata a maboyarta daga baya suka mika ta a hannun ’yan sanda inda yanzu take fuskantar bincike.