Jam’iyyar APC ta ce wadanda suka sanar cewa ta dakatar da shugabanta na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a mazabarsa, ba mambobinta ba ne.
Sanarwar da shugabannin jam’iyyar na mazabar Ganduje da Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta yi zargin cewa jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar ne ta dauki nauyin wadannan ke ikirarin dakatar da Ganduje.
A ranar Litinin ne shugabannin APC a mazabar Ganduje suka sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.
Amma a wata sanarwa da shugaban APC na karamar hukumar Dawakin Tofa, Ahmed Mohammed Koko da wasu masu ruwa da tsaki suka fitar daga baya sun bayyana cewa, “mun samu takardun shaidar zaman da masu ikirarin sallamat Ganduje suka yi da NNPP.
- Ba na son zama uban gidan kowa a siyasar Kaduna — El-Rufai
- Zargin Rashawa: APC ta dakatar da Ganduje
Kilo ya ce jam’iyyar “ta gano wadanda suka yi wannan aika-aika kuma za ta maka su a kotu kan zargin yin sojan gona.”
Wasu ikirarin su ne shugabannin APC a mazabar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa suka sanar da shi a wani taron ’yan jarida.
Dai dai ba a jima ba shugabancin jam’iyyar ya yi watsi da sanarwar farkon tare da dakatar da wadanda suka fitar da ita.
Shugaban APC na karamar hukumar, Inusa Dawanau, ya zargi masu sanarwar dakatar da Ganduje da yi wa jam’iyyar zangon kasa, kuma an bankado takardun da ke tabbatar da zaman da suma yi da jam’iyyar adawa.
Tuni da dai shugabancin APC ya tabbatar da dakatarwar wata shida da aka yi wa jami’an da aka gano.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas ya kara da cewa an kafa kwamitin bincike kan badaƙalar.
Sai dai daya daga cikin waɗanda ake zargin, Halliru Gwajo, ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje ne kan zargin karbar rashawa da gwamnatin Kano ke masa.
Ganduje dai ya sha musanta zargin.