Majalisar Wakilai ta koka da rashin tsaron da ke addabar yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan kasar nan, lamarin da ta bayyana a matsayin wata barazana ga Najeriya sakamakon illar da hakan ke haifarwa wajen samar da abinci a kasar.
Ta ce, rashin tsaron da aka kwashe sama da shekaru 10 ana fuskanta ya haifar da mummunan yanayin da ake fama da shi a Najeriya.
Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu ne ya bayyana hakan yayin jawabin bude zaman zauren majalisar na wannan Talatar.
A cewar Benjamin Kalu, ƙarancin abinci ya shafi zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin barazana mai girman gaske ga zaman lafiya da dorewar Najeriya.
Ya ce, “Hauhawar farashin abinci, babban kalubale ne ga Najeriya wanda alkaluma suka nuna ya kai kashi 35.41 cikin 100 a watan Janairun 2024.
“Wannan wani nauyi ne mai girman gaske ga al’ummar Najeriya a yayin da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce, kashi 90% na ‘yan kasar na ware kashi 60% na abin da suke samu don biyan bukatunsu na yau da kullum.
“Wannan mummunan lamari ya kara dagula al’amura, kuma wata alama ce mai ban tsoro a wannan shekarar 2024.”
Kalu ya kara da cewa, “An yi hasashen adadin mutanen da ke fama da ƙarancin abinci zai kai miliyan 26.5, inda yara miliyan 9 ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.”
Benjamin Kalu ya bayyana noma, a matsayin wani bangare mai muhimmanci, yana mai cewa “noma ne bangaren da ke wakiltar kashi 23% na ɗaukacin abin da ƙasar nan ke samu, kuma wannan bangare ne da kashi 51% na ‘yan Najeriya suka dogara da shi, kuma shi ne ke samar da abinci.”