Erik Ten Hag ya bayyana dalilin da ya sa Manchester United ta ɗauko aron Sofyan Amrabat da rawar da zai taka a kungiyar a bana.
Ɗan kwallon tawagar Morocco zai buga gasar Premier daga Fiorentina, bayan da ya koma Old Trafford ranar Juma’a ranar karshe da aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai.
- An bude sararin samaniyar Nijar bayan wata guda da juyin mulki
- Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan Zaben 2023
Amrabat bai cancanci buga wasan da Arsenal ta ci Man United 3-1 a Premier League ranar Lahadi ba, saboda ba a sanar da lambar rigar da zai saka ba har sai an kammala kulla yarjejeniya.
Ten Hag ya sanar da cewar ”Yana cike da murna” da suka ɗauki aron ɗan kwallon mai shekara 27, kuma zai kara karfin kungiyar.
A hira da ya yi da ‘yan jarida a Emirates bayan karawa da Arsenal, Ten Hag ya ce ”Ciniki ne na farkon kakar bana da nake fatan samun mai buga tsakiya ɗaya daga gurbin da muke bukatar kara karfi.”
”Casemiro ne kaɗai muke da shi da yake taka rawar gani a gurbin , kenan mun kara samun wani wato Sofyan Amrabat mai sa kwazo sosai.”
”Haka kuma zai iya buga tamaula tare da Casemiro, saboda yana iya zuwa gaba sosai. Saboda haka mun yi dace da muka same shi – ina jin abu ne mai kyau ga Premier League da Champions League. Ana buƙatarsa yadda ya kamata.”
”Yana da kyau sosai yana da kwarewa wajen gogayya da abokin hamayya, ina ganin zai taka rawar gani a ƙoƙarin da muke na komawa kan ganiya.
Kawo yanzu Manchester United ta ci wasa biyu an kuma doke ta karawa biyu, inda take da maki shida sannan a mataki na 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.