Majami’u ko coci-coci na ci gaba da samun koma-baya a kasar Amurka, inda ake rufe da yawa daga cikinsu.
Masu bincike sun ce, hakan na faruwa ne a kusan dukkan fadin kasar, kuma wannan shi ne koma baya mafi muni da aka taba samu a wannan karni da Amurkawa ke watsi da addinin Kirista a kasar, yayin da kuma ake samun bullar wasu majami’un.
- Hattara da masu yada labaran karya a kan Tinubu —APC
- Ba mu yarda da tsawaita wa’adin tsohuwar Naira ba —Majalisa
Yayin da ake kara samun yawaitar mutanen da ba su da addini a kasar, dubban coci-coci ake ci gaba da rufewa kusan kowace shekara a kasar.
Wannan ya sa dole malaman coci-coci suka canza shawara ta daina taron addu’a, kuma suka sa majami’un a kasuwa.
Kimanin majami’u 4,500 ne aka rufe a shekarar 2019, ana samun bayanan shekarar da ta gabata, tare da kusan sababbin majami’u 3,000 da aka buɗe, a cewar Binciken Lifeway.
Wannan ne karon farko da adadin majami’u a Amurka ba su karu ba tun lokacin da wani kamfanin bishara ya fara nazarin batun.
Barkewar cutar Coronavirus ta kara habaka yawan Amurkawa da ke bijire wa addinin Kirista.
“Rufe majami’u na wani dan lokaci, a dalilin cutar Coronavirus ya shafi majami’u da yawa.
“Mutane da yawa sun daina damuwa da zuwa coci, wanda hakan na nufin yawancin majami’u dole su tashi tsaye don shawo kan mabiyansu su dawo don su rika halartar cocicocin,” in ji Scott McConnell, Babban Darakta a Kungiyar Bincike ta Lifeway.
“A cikin shekara uku da suka gabata alamu suna nuna ana ci gaba da saurin rufe majami’u mai yiwuwa kama da 2019 ko kuma mai yiwuwa sama da haka, saboda da gaske an samu karuwar Amurkawa wadanda suka ce ba su da addini,” in ji shi.
Malaman coci ’yan Furotestan sun ba da rahoton cewa yawan masu halartar majami’u ya ragu da kashi 85 a cikin wadanda suka kamu da cutar Kwarona, in ji McConnell, yayin da binciken da Cibiyar Bincike kan Rayuwar Amurka da Jami’ar Chicago ya gano cewa a bara, kashi 67 na Amurkawa sun ba da rahoton zuwa coci sau daya kacal a shekara, idan aka kwatanta da kashi 75 kafin barkewar cutar Kwarona.
A lokacin da cutar Kwarona ta habaka an samu raguwar masu zuwa majami’u sosai.
A 2017 wani bincike da cibiyar Lifeway ta gudanar ya gano cewa matasa masu shekara tsakanin 18 zuwa 22 da suke zuwa coci a-kai-a-kai, ba su da yawa, idan aka kwatanta da masu halartar makarantar sakandare.
Kamfanin ya gano cewa mutum 7 cikin 10 sun daina zuwa coci kamar yadda suka saba yi a-kai-a-kai.
Binciken Scott McConnell A cewar Scott wasu daga cikin dalilan da suka sa matasan ke kaurace wa zuwa coci sun hada da tafiya babbar kwaleji, ko fara aiki wanda ya sa ya zama da wahala su iya zuwa coci.
Kashi daya cikin hudu na matasan da suka daina zuwa cocin sun ce ba su yarda da matsayin cocinsu kan batutuwan siyasa da zamantakewa ba, in ji McConnell.
Wani bincike da Cibiyar Pew Research ta gudanar ya gano cewa adadin Amurkawa Kirista ya kai kashi 64 a shekarar 2020, tare da kashi 30 na yawan jama’ar Amurka a matsayin “marasa alaka da kowane addini.”
Sai kuma kashi 6 na Amurkawa da suke bin addinin Yahudanci da Musulunci da Hindu da Buddha.
“Tun shekarun 1990, Amurkawa suka fara barin addinin Kirista don shiga cikin manyan Amurkawa da ba su yarda da Allah ba.
A cikin 1972 kashi 92 na Amurkawa suna bin addinin Kirista ne, in ji Pew, amma nan da shekara ta 2070 adadin zai ragu zuwa kasa sosai da kaso 50, kuma adadin Amurkawa “marasa addini” zai iya zarce wadanda ke bin addinin Kirista.
Wani marubuci mai suna Stephen Bullibant, wanda ya rubuta: The Making of Ed-Christian America, kuma Farfesan Ilimin Tauhidin Kiristanci da Zamantakewar Addinai a Jami’ar St Mary, ya ce a duniyar Kirista hakan na iya kasancewa.
Yayin da kakanni za su kasance masu zuwa coci a-kai-a -kai, ’ya’ya da jikokinsu za su ce sun yi imani da Allah ne kawai, amma ba sa zuwa coci a-kai-a-kai.
A dubban shekaru masu zuwa za ka tarar gaba daya ma, ba su damu da yin wata mu’amala ko kulla dangantaka da majami’a ko kuma addini ba.
Farfesa Bullibant ya ce sauran kasashe sun ga yadda aka samu canji daga wani addini zuwa wani kafin Amurka, amma Amurka tana da yanayi na musamman da ke dakile al’amura.
Kasashe irin su “Kanada, Biritaniya, Faransa, Austireliya, New Zealand, sun ga irin wannan canji da yawa a baya.
A shekarun 1960 irin wannan lamari na wasu jama’a da kan bar addini zuwa wani daban’’ in ji Bullibant.
“Abin da ke faruwa a Amurka wanda ina tsammanin ya rage tashin hankali shi ne yakin cacar baka.
Domin a Amurka, ba kamar a Biritaniya ba, akwai wani nau’i na musamman na ‘Kirista a Amurka’ tare da tsarin gurguzu na rashin bin Allah, kuma rashin addini shi ne a wajensu zama Ba’amurke.
“Ina tsammanin hakan ya taimaka har aka kai wani karni na dubban shekaru na bin tsantsar addini da kuma irin tasirin da yakin cacar baka ya yi, wanda har ya zama abin tunawa ga wasu tun daga ƙuruciyarsu,” in ji shi.
Lokacin da mutane ke tafiya majami’u na kara raguwa.
Kuma idan hakan ya ci gaba to zai kasance wani babban batu muhimmin ga koma-baya da tasirin da majami’un suke da shi, wanda dole zai zama a rufe su domin babu masu halarta, wanda wannan lamari ya haifar da karuwar yadda ake sayar da coci-coci da a baya wuraren bauta ne masu tsarki.
Mista Brian Dolehide, Manajan Daraktan Kamfani AD Advisors, wani kamfani na gidaje da ya kware wajen tallace-tallacen coci, ya ce shekara 10 da suka gabata an samu karuwar tallace-tallacen sayar da coci-coci a-kai-a-kai da suke zama gidaje ko gidajen kula da yara, yayin da wasu majami’un ke sayen wasu majami’u suna fadada nasu.
Amma sayar da coci ba kamar sayar da gida ko kasuwa ba ne.
Sau da yawa masu sayarwar suna son mai saye wanda ke shirin yin amfani da cocin don kyakkyawar manufa.
Mista Dolehide ya ce kwanan nan ya sayar da coci a El Paso wanda yanzu ake amfani da shi a matsayin gidan ’yan gudun hijira, haka kuma wasu akan yi amfani da su a matsayin gidaje masu saukin kudi.
Mukan yi mu’amalar cikin ban-gaskiya ba tare da neman wata riba ba.
Ba ma neman riba daga ciniki irin wannan sai dai muna neman mafi kyan wadanda za su yi amfani da su.
Rufewar ba ta yadu zuwa ko’ina a kasar ba. Ko a Jihar Tedas, Mista John Muzyka ya ce akwai karancin majami’u na sayarwa, idan an kwatanta da shekara 15 da suka gabata.
Ya yi imanin cewa hakan na daga cikin irin matakan da aka dauka, bayan barkewar cutar Kwarona, inda Gwamnan Jihar ya ba da izinin a bude majami’u a watan Mayu 2020, duk da yadda aka samu karuwar kamuwa da cutar.
“Idan aka rufe coci fiye da shekara guda, yana da wahala mutanen da ke halartar wannan majami’a su dawo.
“Lokacin da aka rufe ku na wata uku, kun samu damar shawo kan lamarin,” in ji Muzyka.
Baya ga haka,mafi yawan rufe majami’u galibi na faruwa ne saboda gazawar majami’un wajen tafiyar da al’amuransu.
“Idan majami’a ta tsufa kuma ba a kai ga sa matasa a gaba ba, ko kuma aka kasa canza al’amuran tafiyar da ita, akan kai ga rufe ta,” in ji shi.
Hakazalika akan samu matsalar rashin kudin da za a tafiyar da majami’ar, wanda kan kai ga rufe ta.
“Eh, akwai matsin rashin kudin da zai jawo a rufe coci, amma sau da yawa, akan samu wannan matsalar ce ta rashin canza tsari da kuma ba matsa dama, ko kuma cocin ba ya da isassun matasan da za su ci gaba da tafiyar da shi,” in ji shi.
(Madogara: The Guardian)