✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da jirgin soja ya kashe kananan yara a Neja —Gwamnati

Gwamnatin Jihar Neja ta ce a iya saninta babu mutane a kauyen

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ba ta san da zaman mutane ba a kauyen da jirgin soja ya kashe kananan yara shida ya kuma rusa gidaje.

Ta bayyana cewa ba ta zaci mutanen kauyen na Kureba da ke Karamar Hukumar Shiroro sun sun ci gaba da zama a kauyen ba, bayan mamaya da hare-haren ’yan bindiga da suka yawaita a yankin na tsawon lokaci, shi ya sa da jirgin ya ga mutane ya bude wuta.

“A iya sanin gwamnati, babu fararen hula a wadannan yankuna saboda yawaitar ayyukan ’yan bindiga da ya tilasta wa mazauna yankunan tafiya su zama ’yan gudun hijiya a wasu sassan jihar,” inji Kwamishinan Kananan Hukumomi, Masarautu da Tsaron jihar, Emmanuel Umar.

Ya sanar da haka ne a Minna, hedikwatar jihar, lokacin da yake tabbatar da cewa sojin kasa da jiragen yaki na gudanar aikin tsaro a jihar.

Aminiya ta kawo rahoton yadda wani jirgin soja da ke aikin yaki da ta’addanci ya bude wa kananan yara shida wuta bisa kuskure ya kashe su, tare da lalata gidaje a kauyen Kureba, a bisa kuskure.

Kwamishinan ya ce gwamantin jihar ta yi na’am da tsananta hare-haren da sojoji ke yi kan ’yan bindiga a jihohi makwabata da kuma kananan hukumomin jihar da suka hada da Shiroro da Munya da sauransu.

Ya ce kokarin sojojin na samun nasara inda suke hallaka ’yan ta’addar, suka fatattaki wasu tare da kubutar da mutanen da aka yi garku da su a kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro.

A cewarsa, ganin irin nasara da ake samu, gwamnatin za ta ci gaba da wannan aiki domin tabbatar da tsaron rayukan mutanen jihar.