Babbar Kotun Jihar Kano ta dage sauraron shari’ar da ake yi wa dan kasar Chinan nan, Geng Quangrong, kan zargin kisan budurwarsa Ummulkulsum Buhari (Ummita) da wata daya.
A zaman kotun na ranar Juma’a, masu gabatar da kara karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Lawan Abdullahi, sun gabatar da Insifekta Injuptil Mbambu daga Sashen Binciken Manyan Laifuka da ke Bompai, a matsayin shaida na biyar.
Insifekta Ijuptil ya shaida wa kotu cewa a lokacin da suke bincikar wanda ake zargi, ya bayyana musu cewa ya fara sanin marigayiya Ummita ne yayin da ta karbi lambar wayarsa a wajen kawarta mai suna Hanisa, daga nan suka fara soyayya har ta yi alkawarin za ta aure shi.
“Bayan haka ne ya fara kashe mata kudade masu tarin yawa.
“Ya ce ya tura mata wasu kudi Naira miliyan 18 domin ta yi kasuwanci sannan ya saya mata gida na Naira miliyan hudu,” in ji shaidan.
Bayan sauraron su, alkalin kotun, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya sanya ranakun 19 da 20 da 21 ga watan Disamba domin ci gaba da sauraran shari’ar.”