Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai amsa gayyatar da Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi masa ba ne saboda wasu muhimman ayyuka da suka sha gabansa.
Cikin wata wasika da ya rubuta wa NBA, wacce kakakinsa Abdulmumin Jibril ya wallafa a shafinsa na Twitter, Kwankwaso, ya bai wa kungiyar hakuri bisa rashin samun damar halartar taron.
- LABARAN AMINIYA: Har Yanzu A Gidan Haya Nake Zama A Abuja —Shekarau
- Baraka ta janyo dakatar da daukar sabbin ’yan sanda
“Ina so na bayyana cewa na samu wasikar gayyatarku, mai dauke da maudi’in da ya gabata.
“Ina kuma so na sanar da ku cewa ban samu damar halartar wannan taro mai muhimmanci ba, saboda wasu muhimman abubuwa da ke gabana da suka shafi kasa,” a cewar wasikar.
Cikin wasikar, Kwankwaso har ila yau ya ce, abokin takararsa Bishop Isaac Idahosa ya fita kasar waje, “amma da na turo shi don ya wakilce ni.”
A ranar Litinin kungiyar ta NBA ta gudanar da Babban Taronta na kasa a karo na 62 a Otel din Eko Hotels and Suites da ke yankin Victoria Island a Jihar Legas.
Taron ya samu halartar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi.
Kamar Kwankwaso, shi ma dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Ahmed Tinubu, bai samu halatar taron ba, amma ya tura abokin takararsa Kashim Shettima wanda ya wakilce shi.