Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana cewa a yanzu ba za ayi zaben shugabannin kananan hukumomin jihar da aka dakatar ba, saboda gudun sake fadawa, cikin rikici.
Gwamna Lalong ya bayyana haka ne wa ’yan jarida a garin Jos, lokacin da yake magana kan zaben kananan hukumomin da suka hada da Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Barikin Ladi da Riyom, da ba yi ba.
- Wata mata ta yi wa kishiyarta duka da tabarya, ta banka mata wuta
- Masu Keke Napep sun shiga yajin aiki a Maiduguri
- ‘Ana fakewa da sunan rikicin makiyaya don a raba kan Arewa’
“Ya kamata mutane su fahimci cewa jihohi kusan takwas a Najeriya ba su yi zaben kananan kukumomin ba, kuma ba su bayar da dalilansu na kin yin zaben ba. Misali kamar Jihar Anambara, an kai shekara rabon da a yi zaben kananan hukumomi,” inji Lalong.
Ya yi bayanin cewa za a iya yin kowanne irin zabe a Jihar Filato ba tare da samun wani rikici ba, amma idan aka tashi yin nan kananan hukumomi akan samu rikici, saboda shi ne yafi kusa da jama’a.
Ya ce a baya an yi zaben a jihar kuma jam’iyyun adawa suka ci, aka kuma ba su.
“Amma a makwabciyarmu Jihar Bauchi, kwanakin baya an yi zaben kananan hukumomi, abin mamaki ko kansila daya, babu jam’iyyar adawa da ta samu. To mu haka ba za ta yiwu ba a Jihar Filato.
Ya bayyana cewa, “A nan Jihar Filato rikici na iya tashi a kan zaben kansila, har ta kai ga kashe-kashe, Mu kuma zaman lafiya muke so a jihar nan.”
Ya ce, “Rahoton da jami’an tsaro suka kawo mana ya nuna cewa babu tabbacin idan muka yi zabe a wadannan kananan hukumomi ba za a samu rikici ba.
“Hatta ’yan kasashen waje suna zuwa suna ce mana mu yi taka-tsantsan da yin zaben kananan hukumomi a yanzu, domin yanzu muna neman mutane ne daga waje don su zo su zuba jari a Jihar nan.
“Don haka zaman lafiyar da muka samu ne a jihar muke riritawa, ba ma son mu sake komawa gidan jiya da suna zaben kananan hukumomi.
“Idan kuma muka samu rahoton cewa mu shirya zaben nan, babu wata matsala, za mu yi,” inji shi.