✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da aka kai samame gidan Matawalle — Gwamnatin Zamfara

Har kayen lefen da aka kawo wa diyata an kwashe, a cewar Matawalle.

Gwamnatin Zamfara ta ce da umarnin Kotu aka kai samame tare da kwashe motoci 40 a gidan tsohon gwamnan jihar, Muhammed Bello Matawalle.

Gwamnatin na wannan kalamai ne a matsayin martani ga Matawalle da ya zargi Gwamna Lawal Dauda Dere da jagorantar afka wa gidansa aka kwashi motoci.

A wata hira da ya yi da BBC, tsohon gwamna, Bello Matawalle ya yi zargin cewa baya ga kwashe motocinsa na hawa an kuma wawushe dakunan matansa tare da zargin cewa Gwamna Dauda ne ya jagoranci samamen.

Matawalle ya ce an kwashe har murahun girki da kayan lefen da aka kawo wa diyarsa da yake shirin aurarwa.

Sai dai, babban mai ba gwamnan Zamfara shawara kan harkokin watsa labarai Mustapha Jafaru Kaura, ya shaida wa BBC cewa ce jami’an tsaro ne suka kai samamen a gidan tsohon gwamnan bayan samun umarnin kotu.

“Umarni aka bayar ko can baya, an je wurin kotu kuma ta ba da umurni aje gidansa na nan Gusau, da kuma wanda ke Maradun domin a dauko motocin”.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce duk motocin da aka dauko daga gidan tsohon gwamnan, na gwamnatin ne.

Ta kuma karyata zargin da Matawallen ya yi kan cewa an dauki motoci masu dauke da hoton shi da Shugaba Tinubu.

Sai dai tun farko Matawallen ya musanta ikirarin da mahukutan jihar suka yi kan cewa adadin motocin da suka dauko ya kai 40, kuma akasarinsu motocinsa ne da ya sayo da kudinsa a Amurka.

A yanzu mahukunta jihar sun ce ’yan sanda ne suka kirga motocin bayan da aka daukosu.

Sun kuma karyata ikirarin da Matawalle ya yi a kan cewa jami’an tsaro ne su ka kai samamen gidansa karkashin jagoranci kwamishinan ’yan sanda da kuma sabon gwamnan jihar, Lawal Dare.

“Me Dauda Lawal zai je ya yi a gidan shi? Me ya hada Dauda Lawal da zancen daukar mota?” in ji Mustapha Jafaru.

Ka kawo mana shaidar motocinka ne — ’Yan sanda ga Matawalle

Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta fitar da wata sanarwa ita ma, tana mai cewa za ta ci gaba da bincike da kwato motocin gwamnatin da aka zargin tsohon gwamnan da sace wa.

Sanarwar da ’yan sandan ta ce duk wanda yake ganin an karbe motarsa ba ta gwamnati ba ce, to ya kawo takardar shaidar cewa motarsa ce a mayarsa masa.

Wannan dambarwa tsakanin tsohon gwamna da bangaren sabuwar gwamnati ta ja hankalin jama’a, musamman zarge-zarge da Matawalle ya yi bayan afkawa gidansa.

Tun kafin wannan lokaci gwamnan Lawal Dere ya ke ta sanar da cewa Matawalle ya wawushe dukiyoyin gwamnati da motoci inda aka bukaci ya gaggauta mayar da su.

Sai dai Matawalle ya yi biris yana mai cewa ana yi masa bita-da-kullin siyasa, lamarin da ya tilasta kai wannan samame bayan gargadi da aka rinka fitarwa a kansa.