Manoman zobo a Jihar Katsina sun koka bisa yadda zobon bai yi kyau ba a daminar bana, duk kuwa da yake an samu isasshen ruwan sama.
Kamar yadda manoman suka ce, rashin samun taki mai rahusa a kan kari a farkon damina da kuma mamaye gonakinsu da wasu makiyaya daga kasar Nijar suka yi suna daga cikin dalilan da suka haddasa rashin albarkar zobo a bana.
Wani dalilin kuma da manoman suka alakanta da tauye ci gaban kasuwar zobon shi ne na yadda mahukuntan Karamar Hukumar Mashi suke ta canza wa kasuwar zobo matsuguni nesa da babbar kasuwar garin Mashi.
Haka kuma manoman sun lura cewa yawan ruwan sama da aka samu daga karshen daminar bana ya sanya zobonsu bai yi tsayi sosai ba ta yadda zai iya haihuwar ’ya’ya kwatsa-kwatsa wadanda filawar jikinsu ce ake kira zobo.
Matsalolin da harkar zobo ta fuskanta
Malam Abdullahi Kwangwama, sanannen manomin zobo ne a Karamar Hukumar Mani, a hirarsa da Aminiya ya bayyana cewa tun a farkon daminar bana gwamnati ba ta ba su takin zamani ba.
Ya ce: “Sam ba mu samu taki daga hannun gwamnati ba a bana; haka ne ya sanya zobonmu ya tsumbure.
“Daga baya mun samu sayen taki a kan Naira dubu 12 kowane buhu don haka ne zobo bai samu ya yi tsayin da zai kama kirji ba kamar yadda ya saba.
“Hakan kuma na nufin bai samu sukunin zuba ’ya’ya kwatsa-kwatsa ba.
“A bana ban noma hatsi sosai ba, ga shi kuma zobon bai yi kyau ba; Buhu 60 kawai na samu sabanin buhu 85 da na samu a kakar bara.
“Ka ga kuma ina da mata biyu da yara takwas kuma shida daga cikinsu suna zuwa makaranta da kudin zobon nan nake sa ran zan ciyar da su kuma in biya musu kudin makaranta.”
Yadda za a bunkasa noman zobo
Da yake bayani a kan fatan da manoma zobo suke yi a kan samun ci gaban noman zobo a fadin jihar, Kwangwama cewa ya yi: “Idan har gwamnati na son taimaka mana mu noma isasshen zobo wanda kamfanoni na ciki da wajen kasar nan za su saya, ya kamata ta yi tanadin takin da za ta rinka sayar mana da wuri sannan ta tallafa mana da bashin da babu ruwa don mu yi aron gonakin da za mu fadada noman zobo.
“Domin kuwa zobo yana da masaya haka kuma mu ma a shirye muke wajen inganta nomansa.”
Amfanin zobo
Shi dai zobo ana amfani da shi ne a nan Najeriya wajen samar da abin sha da kowa ya sani da zobo, wanda masana suka ce yana taimaka wa masu fama da ciwon ciki da masu hawan jini da kuma masu son rage kiba.
A wasu kasashen ketare kuwa ana amfani da zobo a masana’antun hada magunguna da masaku da kuma masana’antun kayan alatu.
‘Gwamnati na mana rikon sakainar kashi’
Shi ma da yake bayani wani falke kuma manomin zobo kuma mai suna Ali Makeri ya koka ga irin yadda mahukuntan Karamar Hukumar Mashi ta Jihar Katsina suke yawan canza wa kasuwar zobo matsuguni wanda ya ce hakan yana tauye ci gaban kasuwanci zobo a yankin.
Makeri ya ce: “Duk da yake muna samar wa gwamnati kudaden shiga tare da biyan haraji da kuma sama wa jama’a ayyukan yi, amma a kullum sai ka ga jami’an Karamar Hukumar Mashi sun dauke mu daga wannan jeji sun mayar wancan.
“Kuma da zarar sun ga mun raya inda suka mayar da mu sai su kara zuwa su canza mana wuri. An yi mana haka kusan sau biyar ke nan.
“Na baya bayan nan shi ne suka kawo mu nan gefen sabuwar kasuwar zamani ta Mashi da aka gina suka jibge mu.
“Wannan yana tauye ci gaban kasuwar zobo a yankin ganin cewa mafi yawan masu zuwa sayen zobon suna zuwa ne daga sassa daban-daban na kasar nan.
“Kuma ka san ba su samun natsuwar biyo mu zuwa wadannan wurare da suka yi nesa da babbar kasuwar Mashi saboda dalilan tsaro.”
Da yake karin bayani a kan ko manoman zobo na Jihar Katsina na da yawan da za su iya noma wadda za a iya fitar wa wasu kasashe? Makeri cewa ya yi: “Me kuwa zai hana, noman zobo yana da riba kuma akwai daruruwan manoma zobo a fadin jihar nan.
“Ko a bara a farkon kaka mun sayar da buhunsa kan dubu takwas amma zuwa bazara sai da ya kai har Naira dubu 20.
“Idan da a ce gwamnati za ta samo wani kamfani ya zo ya yi sansani a nan yadda da mun girbe zobonmu sai kawai mu kawo da za mu iya ninka abin da muke samarwa a yanzu. Ta yadda ita kanta gwamnatin za ta rinka samun harajin.”
Abin da gwamnati ta ce
Da yake mayar da martini a kan zargin da ake yi wa Karamar Hukumar Mashi na yawan canza wa kasuwar zobo matsuguni, babban jami’i a Hukumar Noma ta Karamar Hukumar Mashi, Malam Bashir Sanda cewa ya yi: “Gaskiya ne an canza musu matsuguni ba sau daya ba.
“Amma wannan na faruwa ne saboda har yanzu ba su da wurin zaman na dindindin a cikin babbar kasuwa.
“Sai dai gwamnati na nan tana kokarin samar musu da wurin zaman duba da yadda suke sama wa mutane aikin yi da kuma kudaden shiga wa gwamnati.”
‘Makiyaya daga Nijar sun hana ruwa gudu’
Haka kuma wani manomi mai suna Malam Yusuf Gwani Gobirawa da yake a Karamar Hukumar Kaita ya yi korafin yadda wasu makiyaya daga Jamhuriyar Nijar suka tura musu bisashe cikin gonaki wanda ya sanya ba su samu zobo da yawa ba a bana.
Malam Yusuf ya ce: “Zobonmu bai gama nuna ba sai muka ji labarin makiyaya daga Jamnhuriyar Nijar sun fara mamaye gonakin makwabtanmu.
“Jin haka ya sanya dan majalisa mai wakiltarmu a Zauren Majalisar Jiha ya sanya baki ya shiga tsakani ta hanyar Sarakunan gargajiya, inda nan da nan aka ba mu umurnin mu girbe duk abin da ya yi saura a gonakanmu don kauce wa tashin tashina.
“Wannan ne sanya ba mu samu zobo da yawa ba a bana. Duka buhu 45 na samu sabanin buhu 70 da nasa rai zan samu a bana.”
Ya ci gaba da cewa: “Ka ga kan iyakokinmu haka suke sakaka, ya kamata gwamnati ta rinka sa ido kan makiyaya masu shigo mana daga Nijar tun kafin mu kawar da amfanin gonarmu.”
Da yake korafi kan matsalar taki, malam Gwani cewa ya yi: “Ka san da mun dogara ne kan takin gargajiya da shanunmu ke samarwa, ta yadda mukan dauki shanun mu ajiye kamar mako biyu a gonakanmu.
“To yanzu tsoron barayin dabbobi ya hana mu mu kai su nesa da gidajenmu.
“Kai ko da a gidan ma ba ma barci ido rufe domin gudun kada a zo a kore mana su.”
Ana samun zobo mai yawan gaske a kasuwannin Dankama da Mashi da kuma Mai’Aduwa duk a Jihar Katsina.
A yanzu ana sayar da buhun zobo a Naira dubu shida zuwa shida da dari biyar; amma ana sa ran zai iya kaiwa har Naira dubu 20 nan gaba.