A yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da ke Kano ce ta lashe gasar rukunin firmiya na kasa har sau uku a jere. Da wannan nasara da kungiyar ta samu, ta kafa sabon tarihin da babu wata kungiyar kwallo da ta taba yin irinsa a Najeriya. Hatta Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta aika wa kulob din sakon taya murna a kan wannan nasara da ya samu. Sai dai da yawa ba su san dalilin da ya sa kulob din ya samu wannan nasara ba amma wakilinmu Ahmed Garba Mohammed ya lalubo mana wasu daga ciki don amfanin masu karatunmu da kuma magoya bayan kulob din kamar haka:
1. Kulob din yana biyan hakkokin ’yan wasansa a kan kari: daya daga cikin abin da ya sanya kulob din Kano Pillars yake samun nasara shi ne yadda ya dukufa wajen kyautata wa ’yan kwallonsa da jami’ansa musamman wajen biyansu albashi da alawus-alawus dinsu a kan kari. Rahoton da ya fito daga kulob din ya nuna mafi karancin albashin dan kwallo a Pillars shi ne na Naira dubu 200 wanda ya yi daidai da Dala 1,200.
2. Rike ’yan kwallonsa ba tare da sun canza sheka ba: Abin da ya kara daukaka martabar Pillars wajen samun nasara a ’yan shekarun nan shi ne yadda kulob din ya yi kokarin rike ’yan kwallonsa ba tare da sun canza sheka zuwa wani wuri ba. Hakan ya taimaka musu wajen gane kansu a duk lokacin da wasa ke gudana. Kulob din ya samu nasarar rike ’yan kwallo irin su Gambo Mohammed da Rabi’u Ali da Theophilus Afeloka da Shagari Mohammed da Umar Zango da sauransu. Hakan kuma ya taimaka wa masu horar da kulob din wajen horar da ’yan kwallon cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba, tun da ’yan kwallon sun dade suna wasa tare kuma hakan ya taimaka musu wajen gane junansu.
3. Mahukunta kulob din ba sa yi wa koci katsalanda: Wani babban al’amarin da ya taimaka har kulob din Pillars ya yi fice wajen samun nasarori shi ne yadda ake sakarwa duk kocin da ke horar da ’yan kwallon mara ba tare da mahukunta kulob din sun yi masa katsalanda ba, musamman a wajen zaben ’yan kwallon da yake ji zai yi amfani da su a kowane lokaci. A kowane lokaci kulob din yakan ba koci damar sayo zaratan ’yan kwallon da zai yi amfani da su a kakar wasa da kuma wadanda zai yi amfani da su a kowane wasa ba tare da an sanya masa baki ba. Hakan ya taimaka matuka wajen samun nasara ga kulob din na Pillars kamar yadda ake gani a halin yanzu.
4. Sayo zaratan ’yan kwallo: Wani abu da ya kara daukaka martabar Kano Pillars wajen samun nasara a wasanni shi ne yadda kulob din ya sayo zaratan ’yan kwallon da suka taimaka masa. Alal misali, kulob din ya sayo Adamu Hassan daga kulob din Kwara United a bara inda dan kwallon ya ba marada kunya a kakar wasa ta bana bayan ya zura kwallaye 14 a raga. Sannan kulob din ya sayo wasu zaratan ’yan kwallon da suka hada da Ubong Ekpai daga Akwa United da Azeez Shobowale da Eneji Otekpa da kuma Philip Auta da dukkansu suka yi kokari a kakar wasa ta bana wajen taimaka wa kulob din lashe gasar firimiya a karo na uku a jere.
5. Gwamnati tana saka wa ’yan kwallon a duk lokacin da suka samu nasara: Ganin yadda gwamnatin Jihar Kano, karkashin Gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso take sakawa ’yan kwallon da kyaututtuka iri-iri da suka hada da ba kowanensu mota a duk lokacin da suka samu nasara ta sa ’yan kwallon zage damtse don ganin sun cigaba da ba marada kunya a kodayaushe. Kenan, ’yan kwallon kan mayar da hankali wajen samun nasara don sun san akwai kyaututtukan da za su biyo baya daga gwamnatin jiha. Kwamishinan da ke kula da harkar wasanni na Jihar Kano Alhaji Abubakar danburan Nuhu ya ce yadda kulob din na Pillars ya lashe kofin premier na kasa sau uku a jere ya nuna cewa lallai gwmanatin jiha na bayar da gagarumar gudunmawa ga kulob din na Pillars don haka ya yaba wa Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso a kan taimakon da yake yi wa kulob din na Pillars. Hausawa dai kan yi karin magana da “Yaba Kyauta Tukuici”