A ranar Alhamis, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato, ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin yi masa karin haske kan yanayin tsaro a yankin Arewa.
Gwamna Lalong yayin amsa tambayoyin manema labarai na fadar Shugaban Kasa, ya ce ya kuma sanar da Shugaba Buhari a kan shirin gudanar da bikin baje kolin al’adu na kasa (NAFEST) a jihar Katsina da ta kasance mahaifa ga Shugaban Kasar.
Yayin da ya ke jawabi a kan rushe rundunar tsaro ta SARS, Gwamnan ya ce bukatar da ta dace ita ce yi wa rundunar kwaskwarima domin inganta harkokinta na gudanarwa.
A cewarsa, ba dukkanin jami’an rundunar bane bara gurbi, domin kuwa ta kunshi jami’ai masu jajircewa da aiki a kan tsari kamar yadda doka ta tanada.
Ya yi gargadin cewa kada a juya wa rundunar baya domin kuwa yankin Arewacin Najeriya ya ribaci tasirinta wajen magance matsalar tsaro da ta addabi yankin.