Dalibar nan da ta amsa cewa ta kara wa kanta maki a matsayin wacce ta fi kowa a Jarrabawar Neman Gurbin Karatu a manyan Makarantu na Najeriya (UTME) ta bana ta nemi gafarar hukumar JAMB wacce take shirya jarrabawar.
A kwanakin baya ne labarin dalibar, mai suna Mmesoma Ejikeme, ya karade kafafen sada zumunta da ma na yada labarai a Najeriya a matsayin wacce ta fi kowa yawan maki a jarrabawar ta bana.
- Majalisa za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama
- Amarya ta sha da kyar a hannun ’yan bindiga lokacin da ake kokarin kai ta gidan miji
Sai dai daga bisani hukumar JAMB ta karyata ta, inda ta kuma zarge ta da cewa ita ta kara wa kanta da kanta maki ta haramtacciyar hanya.
A yayin zaman kwamitin da Majalisar Wakilai ta kafa domin binciken lamarin ranar Laraba a Abuja, yarinyar ta nemi gafara tare da cewa ta yi nadama.
Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin dan majalisa Sada Soli Jibiya (APC, Katsina) dai ya gayyaci dalibar ne da iyayenta da kuma shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede domin jin bahasi.
Dalibar dai ta halarci zaman kwamitin ne tare da mahaifinta da kuma lauyanta, a inda ta karanta wasikar neman afuwar, ciki har ta amsa laifin da aka zarge ta, tare da neman afuwa.
Tun da farko, Farfesa Oloyede, ya yi bayani daki-daki ta yadda za a iya samun wadanda suke iya canza sakamakonsu da kuma matakan da hukumarsa ke dauka wajen kare hakan, ciki har da hukuncin dakatarwa na shekara uku da ta dauka a kan dalibar.
Ya ce yanzu haka suna kan binciken wasu cibiyoyin jarabawa guda takwas a kan lamarin, inda ya ce an kma wasu ma da suka aikata irin haka, wasu mutum hudu kuma yanzu haka suna kurkuku suna jiran kotu ta yanke musu hukunci.