Gwamnatin Saudiyya za ta bude makarantunta domin ci gaba da darussa daga ranar 30 ga watan Agusta, 2020.
Ministan Ilimi, Hamad Al-Sheikh ya ce dalibai za su rika daukar darussa ne ta intanet daga gida na tsawaon mako bakwai a sabuwar shekarar karatun daga ranar.
“Mun yanke shawarar koyar da daliba a gida daga 30 ga Agusta na makonni bakwai, kafin daga baya mu yanke shawarar fadadawa ko tsawaitawa”, inji shi.
Ministan ya ce daliban manyan makarantu za su ci gaba da daukar darussan zube ta intanet, amma za su hallara a aji domin darussan da suka kunshi gwaje-gwaje.
Al-Sheikh ya ce za a sanar da shafin da dalibai za su rika halartar ajujuwan ta intanet mai suna ‘Madrasati’ nan gaba ta taljibi.
Saudiyya ta rufe dukkannin makarantu da cibiyoyin iliminta a ranar 9 ga Maris 2020 a kokarinta na rage yaduwar cutar coronavirus.
Daga baya ta kaddamar da tsarin karatu ta intanet ya maye gurbin halartar ajujuwa ga dalibai.