✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliban Jangebe sun isa Gidan Gwamnatin Zamfara

Daliban sun isa Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da asubahin ranar Talata.

Daga karshe dai an sako dalibai mata da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar sakandaren kwana ta mata zalla da ke Jangebe, Jihar Zamfara.

Da misalin karfe biyar na asubahin ranar Talata ne daruruwan ’yan matan suka isa Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara bayan ’yan bindigar sun sako su.

Da yake wa daliban jawabi bayan karbar su, Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya bukace su da su dauki abin da ya same su a matsayin kaddara, kuma makiyansu sun ji kunya.

An kubuto daliban ne kwanaki kadan bayan aikin da jami’an tsaro har da jiragen saman ’yan sanda sun yi ta kai koma a sama da kasa karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan Zamfara, Abutu Yaro.

Daga Jangebe an yi na karshe —Buhari

Bayan sace daliban, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce garkuwa da daliban makarantar zai zama na karshe a Najeriya.

Buhari ya kuma yi wa ’yan bindiga kashedi cewa ba su gagari gwamnati ba, domin tana duk abin da ya kamata na murkushe su cikin dan lokaci ba don gudun kar a hada da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Tsirfar garkuwa da dalibai a makarantun kwana

Garkuwa da ’Yan Matan Jangebe shi ne irinsa na uku da aka yi a makarantun kwana na mata zalla daga 2014; kuma na biyar da aka yi a makarantun kwana da tsakar dare a Najeriya.

Harin Jangebe shi ne irinsa na uku a wata uku —daga Disamban 2020 zuwa Fabarairun 2021—kuma na biyu a cikin watan Fabrairun 2021.

A daren Juma’a, 26 ga Fabrairu ne mahara dauke da bindigogi cikin motoci suka kutsa makarantar GGSS Jangebe suna luguden wuta, suka dura daruruwan dalibai daga dakunan kwanansu a motoci  suka yi awon gaba da su zuwa inda ba a sani.

Iyayen daliban da aka sace sun rika yanke jiki suna suma da suka isa harabar makarantar bayan samun labarin harin, wadanda ’ya’yansu suka tsallake rijiya da baya kuma suka kwashe su zuwa gida, tare da yin bore ga hukumar makarantar da ta nemi hana su tafiya da ’ya’yan nasu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta ce dalibai 317 ne ba a gani ba bayan harin, yayin da hudu daga cikin ’yan mata suka samu sulalewa daga hannun ’yan bindigar.

Karin ’yan bindiga sun tuba a Zamfara

An kai harin ne ’yan sa’o’i bayan Gwamnatin Jihar Zamfara ta karbi tubar wasu gawurtattun ’yan bindiga, inda suka mika mata makamansu tare da yin rantsuwa da Alkur’ani cewa ba za su koma ga harkar ba.

Daga cikin wadanda suka tuba har da Zakka, dan tsohon madugun ’yan bindiga a Jihar, Buharin Daji.

Tuban nasu da ajiye makamai na zuwa ne makonni kadan bayan wanda ya jagoranci garkuwa da dalibai 344 a Makranatar GSSS Kankara a Jihar Katsina da wasu daga cikin yaransa sun bayyana tubarsu tare da sallama makamansu ga shirin Gwamnatin Zamfara na afuwa da zaman lafiya.

Daliban Jangebe a Gidan Gwamnatin Zamfara bayan masu garkuwa da mutane sun sako su

Sace Daliban Jangebe ya fusata jama’a

Wasu majiyyoyi a garin na Jangebe da ke Karamar Hukumar Talata-Mafara a Jihar ta Zamfara sun ce sai da maharan suka kai wa wani sansanin jami’an tsaro a garin hari kafin suka yi wa makarantar dirar mikiya.

A safiyar Asarar jama’ar garin Jangebe sun yi ayari domin bin sahun masu garkuwa da daliban ba tare da nasara ba.

Harin dai ya fusata al’ummar garin, inda suka rika farmakinmi, har da wasu  ’yan jarida da suka yi zaton jami’an gwamnati ne, kafin daga baya aka shawo kansu.

Sace daliban ya sa Gwamnatin Zamfara rufe makarantun kwanan da ke jihar, yayin da daga bisani ta sanar cewa ta fara tattaunawa da wadanda suka kai harin, kuma daliban an boye su ne a dajin Dan Fulani da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar.

A ranar Lahadi wasu rahotanni sun bayyana cewa an sako daliban a safiyar ranar, amma gwamnatin jihar ta karyata, tana cewa tana dai kan tattaunawa da ’yan bindigar.

Sace daliban ya tayar da hankali a sassan duniya inda hukumomi da kungiyoyin kasashe suka la’ance shi a matsayin tauye hakkin yara na neman ilimi, suka kuma bukaci a sako daliban cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ko cutarwa ba.

%d bloggers like this: