Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa daliban da suka rubuta jarrabawar kammala sakandire ta NECO a 2021 sun yi mata raga-raga, inda kaso 95 cikin 100 suka samu nasara a dukkan jarrabawar darussa 9 da suka zana.
Kwamishinan Ilimin Jihar Kano, Alhaji Sanusi Sa’idu-Kiru ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Dabo.
- Jami’a ta soke jarrabawa a Kano saboda yajin aikin ’yan Adaidaita Sahu
- Kotu ta umarci a saki zakaran kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan na zuwa ne a yayin da Alhaji Kiru yake bayyana nasarorin da Ma’aikatar Ilimin Jihar ta samu a shekarar 2021 da ta gabata.
A cewarsa, “A cikin shekarar 2021, daliban mu 89,000 ne suka rubuta jarrabawar kammala sakandare, ciki kuwa 80,000 duk sun samu nasara da akalla matakin Credit a duk darussa 9 da suka zana.
“Wannan babban nasara ce da aka samu, la’akari da cewa mun fi duka jihohin kasar nan yawan daliban da suka rubuta jarrabawar a bara.
Alhaji Kiru ya ce wannan nasara ta kara tabbatar da cewa ilimi yana samun muhimmiyar kulawa karkashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Kazalika, ya ce gwamnati ta kashe akalla naira miliyan 235 wajen biyan kudin jarrabawar daliban.