Daruruwan daliban Jami’ar Jihar Taraba da ke garin Jalingo sun yi zanga-zanga kan rashin biyan malamansu albashin wata 10.
Daliban sun rika kona tayoyi tare da lalata dukkan wata alama ta Jam’iyar PDP da ke mulkin jihar a garin Jalingo, babban birnin jihar.
- Kano 2023: Dalilin ba wa Gawuna takarar Gwamna —Ganduje
- An kori Farfesa daga Jami’ar Amurka kan zanen batancin Annabi
’Yan sanda dauke da bindigogi ne aka tura a sassa birnin da kuma gidan gwamnatin Jihar inda masu boren suka yi kokarin kutsawa amma jami’an tsaron suka hana su.
’Yan sandan suka rika yin harbi a sama kafin su watsa daliban daga hanyar da ta shiga gidan gwamnati.
Su ma sojoji sun shiga aikin kwantar ta tarzomar zanga-zangar, inda suka lakada wa wasu daga cikin daliban duka.
Har zuwa lokacin hada wannan labarin dai kura ba ta lafa ba, kuma wasu daga cikin hanyoyin garin ba sa biyuwa saboda tsoron masu zanga-zangar ko kuma gudun fadawa hannun jami’an tsaro.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa an tura jami’ansu masu yawa domin kwantar da tarzoma.