Gwamnatin Katsina ta yanke shawarar dakatar da Tafsiri da sallar Asham a masallatai da sauran wuraren taruwar jama’a ne bayan wani taron gaggawa da ta yi da masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin addini na jihar.
Gwamnatin ta kuma ba da umarnin dakatar da sallar Juma’a da taron ibada a masallatan Juma’a da majami’un da ke fadin jihar.
Bayan kammala taron ne dai aka fitar da wata sanarwa mai dauke da sa-hannun sakataren gwamnatin jihar Dokta Mustafa Inuwa
Sanarwar ta kuma ce an rufe duk kasuwannan dake suke ci a mako-mako wadanda suka hada da Jibiya, da Charanci, da Mai’aduwa, da Mashi, da Sheme, da Kafur, da Dandume da sauransu.
Sai dai Gwamna Aminu Bello Masari ya ce ba zai rufe jihar baki dayan ta ba, sai dai duk wata karamar hukumar da aka samu bullar cutar zai rufe ta.
Sannan ya kara yin kira ga jami’an tsaro da su kara sa ido a kan iyakokin jihar da sauran jihohi tare kuma da na kananan hukumomin da aka rufe domin ganin cewa ba a bayar da damar cutar ta ci gaba ba da yadauwa ba.
In dai za a iya tunawa an fara rufe karamar hukumar Daura a makon da ya gabata sanadiyar samun mutane hudu ’ƴan gida daya dauke da cutar, sai kuma daga baya aka sake samun mutum guda daga Daurar sai na baya-bayan nan wanda aka samu a Dutsin-ma.